Ranar Talata kotu za ta saurari karar Atiku kan nasarar Tinubu

A ranar Laraba kuma za a ci gaba da sauraron karar da Jam’iyyar LP da dan takararta Peter Obi

Ranar Talata kotu za ta saurari karar Atiku kan nasarar Tinubu

Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta dage zamanta zuwa ranar Talata.

A ranar Tala kotun za ta saurari karar da dan takarar shugaban kasa na Jam’iar PDP, Atiku Abukar da kuma Jam’iyy APM suka shigar na kalubalantar nasarar Bola Tinubu na Jam’iyyar APC a zaben.

A ranar Laraba kuma za a ci gaba da sauraron karar da Jam’iyyar LP da dan takararta, Peter Obi da  kuma jam’iyyar APP suka shigar na kalubalantar nasarar Tinubu a zaben na ranar 25 ga waan Fabrairu, 2023.

A halin yanzu wadannan su ne kararraki hudu da ke gaban kotu, bayan Jam’iyyar AA wadda dan takararta na shugaban kasa shi ne Hamza Al-Mustapha, tsohon dogarin tsohon shugaban kasa na mulkin soji, Janar Sani Abacha, ta janye kararta a zaman na ranar Litinin.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) dai a sanar cewa Tinubu na APC ya lashe zaben da kuri’u 8,794,726.

Wanda ya zo na biyu shi ne Atiku Abubakar na PDP da kuri’u 6,984,520 a yayin da Peter Obi na LP ya zo na uku da yawan kuri’u 6,101,533.

Sai dai duk da haka, Atiku da Obi sun garzya gaban kotun suna neman ta soke zaben Tinubu wanda tuni INEC ta ba shi takardar shaidar zama zababben shugaban kasa.

Shugaban kotun, Mai Shari’a Haruna Tsammani ya ba wa bangarorin da ke shari’ar tabbacin samun adalci.

A halin yanzu dai mako uku ya rage a ranar da Tinubu a matsayiin shugaban kasar Najeriya na 16.