Ranar Talata za a fara dawo da alhazan Najeriya
A ranar Talata, 4 ga watan Yulin nan a za a fara kwaso alhazan Najeriya zuwa gida. Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da cewa ana sa ran kammala kwaso alhazan 95,000 ranar 3 ga watan Agusta. Kwamishinan hukumar mai kula da sufurin jiragen sama, Goni Sanda ne ya sanar da haka a […]
A ranar Talata, 4 ga watan Yulin nan a za a fara kwaso alhazan Najeriya zuwa gida.
Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da cewa ana sa ran kammala kwaso alhazan 95,000 ranar 3 ga watan Agusta.
Kwamishinan hukumar mai kula da sufurin jiragen sama, Goni Sanda ne ya sanar da haka a taron bitar aikin hajjin bana, wanda ya gudana a birnin Makkah.
Alhazai sun fara barin Saudiyya bayan kammala Aikin Hajji
Yadda Faston da ya Musuluntar da mabiyansa 100,000 ya yi Hajjin bana
Tuni dai hukumar ta fara raba wa alhazai manyan jakunkuna, gami da sanarwar fara awon kaya, wanda ta ce nan ba da jimawa ba za a rufe.
Alhazan Najeriya 13 sun rasu
A yayin taron ne shugaban tawagar likitocin Najeriya, Dokta Usman Galadima ya sanar da rasuwar alhazan Najeriya hudu a ranar Arafa, wanda hakan ya kara yawan alhazan da suka rasu zuwa 13