Ranar Talata za a rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kano
Tuni dai Majalisar Dokokin Kano ta tantance tare da amincewa da naɗin Garo a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zai rantsar da Murtala Sule Garo a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar a ranar Talata.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai ba gwamna shawara kan yaɗa labarai, Ibrahim Adam, ya fitar a ranar Litinin.
- NNPCL ya ƙulla yarjejeniyar kammala matatun man fetur na Warri da Fatakwal
- An kashe ƙasurguman ’yan bindiga biyu a Zamfara
Sanarwra ta ce za a gudanar da bikin ne da ƙarfe 11:00 na safe a zauren taro na Coronation Hall da ke Fadar Gwamnatin Kano.
Za a rantsar da Murtala Garo bayan murabus ɗin tsohon mataimakin gwamnan, Aminu Abdussalam Gwarzo ya yi a ranar 27 ga Maris 2026, sakamakon saɓani tsakaninsa da gwamnan da kuma rikicin siyasa.
Tuni dai Majalisar Dokokin Kano ta tantance tare da amincewa da naɗin Garo, wanda a baya ya taɓa riƙe muƙamin kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin masarautu a gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamna Yusuf ya bayyana zaɓen Garo a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa haɗin gwiwar siyasa da kuma faɗaɗa goyon baya a jihar.