Ranar Tunawa da Mazan Jiya
Shekaranjiya Laraba – ta kasance Ranar Tunawa da Mazan Jiya ta shekarar 2020, rana ce da aka ware kacokan domin tunawa da mazan jiya da suka sadaukar da rayukansu domin kasa ta zauna lafiya – sa’annan suka kwanta dama a fagen daga. Rana ce kuma ta zaratan sojojin da ke fafatawa a fagen fama – […]
Shekaranjiya Laraba – ta kasance Ranar Tunawa da Mazan Jiya ta shekarar 2020, rana ce da aka ware kacokan domin tunawa da mazan jiya da suka sadaukar da rayukansu domin kasa ta zauna lafiya – sa’annan suka kwanta dama a fagen daga.
Rana ce kuma ta zaratan sojojin da ke fafatawa a fagen fama – wadanda a wasu lokutan sukan sadaukar da rayukansu domin tabbatar da kare ’yancin kasa da wanzar da zaman lafiya a duniya ta hanyar shiga ayyukan samar da zaman lafiya a karkashin shirye-shiryen Majalisar Dinkin Duniya da dama.
Domin tuna ranar, shugabannin soji na kasa da na ruwa da na sama har ma da mazan jiya da suka ritaya tare da rufa bayan shugabannin siyasa a matakan jihohi da tarayya sukan hallara a makabartar binne mazan jiyan na kasa da jihohi 36 na kasar nan.
Kasancewar biki ne wanda ake jefar tsuntsu biyu da dutse daya – inda akan tuna da mazan da suka kwanta dama da wadanda ke raye, a baya ana gudanar da bikin ne ranar 11 ga Nuwamban kowace shekara domin ta yi dai da Ranar Tunawa da Mazan Jiya da ake kira Poppy Day – ranar da ake girmama mazan da suka kwanta dama a Yakin Duniya na Farko da na Biyu a kasashen Rainon Ingila. Daga baya an sauya ranar zuwa 15 ga Janairun kowace shekara – domin tuna ranar da sojin Biyafara suka mika wuya ga sojojin Tarayyar Najeriya a ranar 15 ga watan Janairun 1970.
Alal hakika, sojoji sun kasance wata kafa guda da ta yi alkawari kuma ta himmatu wajen tabbatar da wanzuwar tsarin doka da oda da kundin tsarin mulki da muke cin moriyarsa a yanzu a Najeriya. Domin wannan dalili ne ya sa a halin yanzu wadannan sojoji na can a fagen daga inda suke gumurzu da ’yan ta’addan Kungiyar Daular Musulunci a Yammacin Afirka (ISWAP) ko Boko Haram da ’yan ina da kisan makiyaya da masu garkuwa da jama’a da sauran miyagun cikin al’umma.
Yadda za a iya fahimtar girman aikin da ke gaban sojojin Najeriyar shi ne idan aka yi dubi da Alkaluman Duniya kan Ta’addanci (GTI), suka sanya Najeriya a matsayin ta uku a zaman kasar da ayyukan tarzoma suka samu gindin zama a duniya – baya ga kasashen Iraki da Afghanistan.
Har yanzu dai shigar sojojin Najerriya ayyukan tabbatar da zaman lafiya da tsaro muhimmi ne ta fuskar dorewar kasar nan – inda take gudanar da irin wadannan ayyuka a jihohi 32 na kasar nan – hakan ya yi daidai da kashi 89 cikin 100 na fadin kasar. A yayin da suke bakin daga ko dai na yaki da Boko Haram ko kuma ma na Samar da Tsaro cikin Kasa (ISOs) da dama cikin zarata sojin kan gamu da ajalinsu ko kuma samun raunuka.
Wadanda Allah Ya yi wa arzikin komawa gida, kan zama magidanta ko ’ya’ya ko ’yan uwan da tunaninsu ya sauya sakamakon yadda suke fuskantar matsalar juyawar kwakwalwa da yaki ke haddasawa. Sun fuskanci mutuwa a a zahiri, sun ga yadda abokan aikinsu ke mutuwa kuma ba su kasance masu iya taimakonsu ba; suna tunanin ma watakila hakan ta faru a kansu.
Alkaluman mace-macen suna tayar da hankali matuka- sakamakon a hukumance sojoji 353 aka bayar da rahoton sun rasa rayukansu a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2010 a yaki da Boko Haram da kuma ISWAP. 47 sun rasu a fagen daga a 2016, 72 a 2017, 127 a 2018, 78 a 2019 sai kuma 12 a banan nan. Sai kuma wadansu 9 da aka kashe a kauyen Sunke a Karamar Hukumar Anka Jihar Zamfara sai wadansu 5 a Jihar Neja da kuma wani guda a Unguwar Yako kan hanyar Buruku a Jihar Kaduna.
Don haka yayin da muke tuna mazan da suka kwanta dama, watakila hanyar da ta fi dacewa wajen tuna da su din ita ce, mu girmama wadanda ke raye a halin yanzu. Kada mu yi banza da su lura da yadda suke sadaukar da ransu wajen kare rayuka da dukiyoyinmu – dare da rana, a lokutan da dama cikinmu suke kara-kaina a harkokin kasuwanci da ayyukan gwamnati da sauran hidindimun rayuwa.
A ranar ta mazan jiya (AFRD), ya kamata ’yan Najeriya su nuna hakikanin halayyar tunawa da wannan rana a zahiri a matsayinsu na ’yan Najeriya kuma jami’ai a rundunar sojin kasar nan – wadanda suka mutu dama wadanda ke raye tare da iyalansu. Bai dace ba abin ya zama bikin shekara-shekara kawai. Ya kamata ya zama martabawa da ganin kimar soji da ayyukan da suke gudanarwa – manyan hafsoshinsu da kurata – ta fuskar tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasa.