Kayatattun hotuna abubuwan da ke wakana a Kotun Koli inda ake yanke hukunci kan takaddamar zaben shugaban kasa na 2023.
A yayin da ake jiran hukuncin karshe kan takaddamar zaben shugaban kasa na 2023 daga Kotun Koli, ga wasu kayatattun hotuna abubuwan da ke wakana a can.
A halin daga ake ciki dai jami’an tsaro sun fara tantance mahalarta gabanin zaman na yau Alhamis.
(Hotuna: Onyekachukwu Obi).
Magoya bayan Tinubu
Dandazon magoya bayan Tinubu dauke da kwalayen nuna goyon bayan gwanin nasu.
Magoya bayan Shugaba Tinubu suna cashewa a yayin da kotun kolin ke shirin fara zamanta.
Mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaron kasa, Malam Nuhu Ribadu, a lokacin da ya isa harabar Kotun Kolin
Ministan Babban Birnin Tarayya, Ezenwo Nyesom Wike, na daga cikin mahalarta. Sai dai har yanzu bai bayyana cewa ya sauya sheka zuwa PDP ba, duk da cewa an samu rikici tsakaninsa da jam’iyyarsa ta PDP kafin Shugaba Tinubu ya nada shi minista.
Jami’an tsaro sun yi cikar kwari, inda suke tantance mutanen da ke da izinin shiga domin halartar zaman shari’ar.
Seyi, dan Shugaba Tinubu a lokacin da ya isa kotun kolin.
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, da mukarrabansa a lokacin da ya iso kotun.
Lokacin da jami’an tsaro ke tantance Shugaban Jam’iyar PDP na Kasa, Umar Iliya Damagu a Kotun Koli.
Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Ganduje gabanin jami’an tsaro su tantance shi ya shiga cikin kotun.