Ranar Wasa: UNICEF ta buƙaci iyaye su ware wa ’ya’yansu lokutan wasa

UNICEF ta jaddada muhimmancin wasa a wajen yara.

Ranar Wasa: UNICEF ta buƙaci iyaye su ware wa ’ya’yansu lokutan wasa

Asusun Tallafawa Ilimin Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF ), ta yi kira ga iyaye da su riƙa keɓe wa yaransu lokutan wasa, don su taso da lafiya da kaifin basira.

Shugabar UNICEF a Kano, Mista Rahama Rihood Mohammed Farah ne, ya yi wannan kira a lokacin bikin Ranar Wasa ta Duniya da UNICEF tare da hadin gwiwar Hukumar Ilimin bai ɗaya ta Jihar Kano (SUBEB,) suka gudanar a Makarantar Firamaren Kwalli.

A cewarsa wannan karo na farko da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar 11 ga Yuni a matsayin Ranar Wasa ta Duniya, wacce kuma za a ci gaba da gudanar da bikin duk shekara.

Har wa yau, ya ce yara suna da haƙƙin yin wasa domin yana taimaka musu don girma da kuma samun lafiyar ƙwaƙwalwarsu.

“Yana da kyau mu fahimci cewa wasa abu ne mai matuƙar muhimmanci ba abu ne na ɓata lokaci ba domin yana taimaka wa yaro ya girma, yana taimaka masa wajen fahimtar karatu tare da sanya shi ya zama mutumin kirki a gaba.

“Haka kuma yana taimaka masa ya zama yana cikin farin ciki da nishaɗi.”

A jawabinsa Shugaban Hukumar Ilimin bai ɗaya na Jihar Kano, wanda ya samu wakilin Mataimakiyar Daraktan Ɓangaren Ayyuka na Musamman, Hajiya Magajiya Usman, ta bayyana cewa wasa na daga cikin harkar koyo da koyarwa.

“Mun sani cewa yin amfani da wasa wajen koyar da yara yana sa yara su gane abin da ake koya musu cikin sauƙi da kuma sauri. Haka kuma abin da suka koya ta hanyar wasa yana ɗaɗewa a kansu ba tare da sun manta ba.”

Shugaban na SUBEB, ya yi kira ga malamai da su ɗauki ɗabi’ar koyar da yara cikin wasa da nishaɗi domin samun cin nasarar harkar koyo da koyarwa a tsakanin al’umma.

Ita ma a jawabinta na godiya Shugabar Makarantar Firamaren Kwalli, Hajiya Hassana Umar Amin, ta gode wa UNICEF da SUBEB bisa irin taimakon da suke bai wa makarantar.

A lokacin bikin yaran makarantar tare da malamansu sun gudanar da raye-raye da waƙe-waƙe.