Ranar ’Yaki da Cin hanci da Rashawa: Rayuwa za ta ci gaba da gurbacewa idan…. – Malaman addinai
Gwamnan Jihar Oyo Injiniya Seyi Makinde da manyan jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) sun yi tattaki a ranar Litinin da ta gabata a Ibadan fadar Jihar Oyo, domin tunawa da ‘Ranar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya.’ A lokacin tattakin ne Gwamnan ya tunatar da jama’a illar cin […]
Gwamnan Jihar Oyo Injiniya Seyi Makinde da manyan jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) sun yi tattaki a ranar Litinin da ta gabata a Ibadan fadar Jihar Oyo, domin tunawa da ‘Ranar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya.’
A lokacin tattakin ne Gwamnan ya tunatar da jama’a illar cin hanci da rashawa inda ya ce, babu wani muhimmin ci gaba da za a samu a kasar da ta kasa yakar cin hanci da rashawa a cikin jama’arta.
Kwamandan Hukumar EFCC, shiyyar Ibadan Mista Friday Ebelo, ya bayyana nasarar da hukumar ta samu ne a bana, inda ya ce an kama mutum 878 da ake zargi da laifuffukan cin hanci da rashawa da zamba cikin aminci an kuma gurfanar da 268 a gaban kotu tare da yanke hukunci ga mutum 171 daga cikinsu.
Ya ce, “Bincikenmu ya kai ga rufe asusun ajiyar banki 1,44 da kwato gidaje 14 da motocin alfarma 56 da wayoyin salula da na’urori masu yawa da tsabar kudi fiye da Naira miliyan 211 da kudaden kasashen Amurka da Ingila da sauransu wadanda kotu ta bayar da umarnin a mayar da su ga Gwamnatin Tarayya.”
Aminiya ta jiyo ra’ayoyi da shawarwarin jama’a kan yadda suke ganin za a iya maganin cin hanci da rashawa kwata-kwata a Najeriya. Ustaz Tahir Zubairu cewa ya yi “Annabi Muhammadu (SAW) shi ne ya fara yin magana a kan yaki da cin hanci da rashawa inda ya tsine wa mai karba da mai bayarwa saboda illar da hakan yake haifarwa na lalacewa da gurbatar rayuwar jama’a.”
Amma kamar yadda al’ummar kasa ta tsinci kanta cikin wani mummunan hali da ake samun cin hanci da rashawa a kowane sashe, to, akwai lalurar da ta zama dole kamar asibiti ko gaban ’yan sanda za ka bayar ne domin ceto wanda yake da lalurar rashin lafiya ko wanda ke tsare inda tsinuwar da Annabi (SAW) ya yi ba ta shafi irin wadannan ba.
“Amma idan al’umma ta koma ga karantarwar addininta wajen yin hakuri da abin da Allah Ya ba ka, shi ne zai sanya albarka da al’amuranmu su ci gaba a rayuwarmu. Amma matukar ba mu koma ga koyarwar addini ba, to a gaskiya za mu ci gaba da kasancewa cikin wahala kuma ba za mu samu nasara ba,” inji shi.
Shi kuwa Rabaran Philp Miyango, cewa ya yi “Cin hanci da rashawa rashin gaskiya ne da ya bayyana tun farkon duniya. Amma maganar Ubangiji ne cewa lokaci yana zuwa da mutane za su fi son duniya da kayan cikinta su manta da Ubangiji. “
“Yanzu maganar Allah ta tabbata cewa tsoron Ubangiji ne farkon ilimi wanda mutane suke gujewa, hakan ne ya yi sanadin karuwar cin hanci da rashawa maimakon ya ragu. Abu ne mai sauki kwarai idan muna so mu yaki cin hanci da rashawa, sai dukkanmu mun koma ga Ubangiji wajen yin aiki da abubuwan da Ya shimfida mana. Idan muka koma ga Allah to a cikin minti daya ba za mu sake tunanin cin hanci da rashawa a rayuwa ba,” inji shi.