Ranar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya

Ranar 9 ga Disamban kowace shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniya don yaki da cin hanci da rashawa.Dalilin ware ranar shi ne a nuna muhimmancin yaki da cin hanci da rashawa, wanda ya zama wajibi idan ana so a cimma muradun karni guda 17 da  majalisar ta tsara wa kasashen duniya. Sai kuma a […]

Ranar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya
Ranar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya

Ranar 9 ga Disamban kowace shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniya don yaki da cin hanci da rashawa.Dalilin ware ranar shi ne a nuna muhimmancin yaki da cin hanci da rashawa, wanda ya zama wajibi idan ana so a cimma muradun karni guda 17 da  majalisar ta tsara wa kasashen duniya.

Sai kuma a jawo kowa a yaki da cin hanci; ya zama mutane sun fahimci muhimmancin yaki da cin hanci da rashawa tare da shiga cikin aikin.

Dole ne a sauya tunanin al’umma masu ganin cewa yaki da cin hanci aiki ne na hukumomin gwamnati ko jami’an tsaro.

Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke fama da matsalar cin hanci da rashawa. Misali, kafin a kafa Hukumar EFCC mai yaki da ’yan damfarar Intanet da safarar kudaden haram, Kungiyar Transparency International mai yaki da cin hanci da rashawa, ta bayyana Najeriya a  matsayin ta biyu a tsakanin kasashen duniya da suka fi kowa cin hanci da rashawa. Amma a rahoton da kungiyar ta saki a shekarar 2018, Najeriya ce ta 144 cikin kasashe 180. Duk da wannan matsayi da Najeriya ke samu, wadansu na ganin har yanzu ba ta sauya zane ba dangane da yaki da cin hanci da rashawa.

Tambaya a nan, ita ce me ke kawo wa Najeriya tangarda dangane da yaki da cin hanci da rashawa?

Idan muka yi la’akari da yadda rashawa ta yi wa mutane katutu, musamman babbar rashawa ta sace makudan kudin gwamnati ta hanyar kwangiloli da sauransu, za mu iya cewa aikin ya yi wa Gwamnatin Tarayya yawa. Najeriya akwai jihohi 36 da kananan hukumomi 774, amma hukumomin EFCC da ICPC da CODE OF CONDUCT BUREAU da sauransu, ba su da isassun kwararrun ma’aikata da kayan aikin da za su iya karade kowane sako da lungu na kasar nan. Wannan ya sa akwai bukatar jihohi da kananan hukumomi su rungumi yakin, kuma su kafa hukumomin yaki da cin hanci da rashawar.

Jihar Kano a yanzu ta ciri tuta wajen yaki da cin hanci da rashawa da yaki da azzalumai. Yau a Jihar Kano akwai hukumar yaki da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafe. Wannan hukuma da aka kafa a shekarar 2008, ba ta fara amo ba sai daga shekarar 2015  lokacin da aka nada, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado a matsayin shugaban hukumar.

Saboda haka ci gaban da hukumar ta samu na da nasaba da mutumin da ke jagorantar hukumar. Misali, cikin ayyukan da ya yi shi ne, na yi wa dokar da ta kafa hukumar garambawul, inda Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi wannan aiki, kuma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu.

Baya ga yi wa dokar hukumar garambawul, Muhuyi Magaji, ya yi garambawul ga bangarori daban-daban na hukumar, ya dauki karin ma’aikata, sannan ana shirya wa wadannan ma’aikata horon kara wa juna sani, lokaci zuwa lokaci. Kazalika ana biyan su albashi da hakkokinsu a kai a kai. Hukumar ta yi nasarar dakile damfarar filaye a fadin jihar, har ta kai an cire Babban Sakatare a wata ma’aikata kuma aka gurfanar da shi gaban kotu.

Hukumar ce ta shiga gaba a badakalar cin hanci da zalunci a kasuwannin Kofar Wambai da Kwari ’Yan tebura, inda ta tabbatar duk wanda ke da rumfa ya samu rumfarsa ba tare da macuta sun kwace sun sayar ba. Wani aiki da hukumar ta yi shi ne na tsabtace rajistar ma’aikatan kananan hukumomi da ’yan fensho, hakan ya sa aka bankado ma’aikata ’yan fensho na boge da dama.

Yanzu haka Muhuyi Magaji shi ne, ke jagorancin shirin OGP, wanda shiri ne da zai sa a gabatar da ayyukan gwamnati bude kuma a bayyane. Kadan daga cikin rukunnan wannan shiri shi ne, aiwatar da dokar da ta ba ’yan kasa damar neman bayanai daga hukumomin gwamnati da shirya jin bahasi game da kasafin kudi da bude ofishin tantance bayar da kwangila da sauransu, wanda Jihar Kano ta cika dukkan wadannan sharudda.

In da a ce sauran jihohi akwai hukumomin yaki da cin hanci da rashawa, da kuma jajirtattun shugabanni kamar Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, to da za a kara samun ci gaba da yawa a bangaren yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Wasu darussa da ya kamata mu koya daga yaki da cin hanci da rashawa shi ne, wanda tsohuwar Ministar Kudi da Tattalin Arziki, Ngozi Okonja Iweala ta zana a cikin wani littafinta da ta wallafa da Ingilishi mai taken “REFORMING THE UNREFORMABLE” da kuma daya littafin mai taken “FIGHTING AGAINST CORRUPTION IS DANGEROUS.”

Ta bayyana cewa yaki da cin hanci  na bukatar samun hadin kan shugaban gwamnati, wato Shugaban Kasa ko Gwamna a matakin jiha. Na biyu, ana bukatar a takaita yakin a kan cin hanci wanda ya fi hadari, wanda shi ne, na satar kudin gwamnati.

Na uku shi ne a fito da hanyoyin tantance nasarorin da ake samu a yakin, sai na hudu shi ne, ana bukatar, jajirtaccen mutum wanda bai da tsoro, wanda barazana da bude idanu ba za su tsorata shi ba kuma ba za su sanya ya yi kasa a gwiwa ba. Kazalika, ta bada wasu shawarwari cewa, yana da kyau a samu sadarwa da sakin bayanai a kan nasarori da kalubale da ake samu ta hanyoyin kafafen watsa labarai da kuma shirya tarurrukan wayar da kai.

Kazalika, ya kamata a shigo da kungiyoyin farar hula da na jama’a a cikin yaki da cin hanci ko kawo wani sauyi a gwamnati. Okonja Iweala, wadda a lokacinta ne aka shimfida duk wasu tsare-tsare na sauyi a Najeriya ciki har da buga kudaden da ake bai wa jihohi da kananan hukumomi a jaridu da kirkirar asususn tara kudin rarar man fetur (ECR) da shigo da sabon tsarin fansho da sauransu ta ce yaki da cin hanci da rashawa abu ne mai hadari.

Ta ma danganta yadda saboda jajircewarta ya sa masu amfana da tallafin mai suka kitsa yadda aka sace mahaifiyarta, aka yi garkuwa da ita da sharadin sai ta yi murabus daga mukaminta na Minista sannan za a sako mahaifiyar, abin da ta ki yi, daga karshe aka biya makudan kudin fansa sannan aka sako ta.

Abin da ta fada ya yi daidai da abin tsohon Shugaban Hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribadu ya ce idan kana yaki da cin hanci da rashawa, to shi ma zai yake ka. Kazalika, Barista Muhuyi Magaji Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa ta Jihar Kano, ya ce yaki da cin hanci da rashawa ya fi komai wahala musamman a matakin jiha.

Wannan ya sa ya zama wajibi a matsayinmu na ’yan kasa nagari, mu bai wa dukkan mutanen da aka ba jagorancin hukumomin yaki da cin rashawa cikakken hadin kai. Aikinsu na da hadari, kuma ba kudin da za a iya biyansu. Mu sani yaki da cin hanci da rashawa na kowa da kowa ne. Ni da kai da ke da kowa ma.

Kwamared Bishir Dauda, Sabuwar Unguwa Katsina Babban Sakataren Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa, kuma Daraktan Kungiyar Yaki da Cin hanci ta c-pac.  08165270879