Ranar ’Yanci: Jihar Borno ta takaita bikin zuwa addu’o’i

Sakamakon mummunan ambaliyar ruwa a birnin Maiduguri da kewaye

Ranar ’Yanci: Jihar Borno ta takaita bikin zuwa addu’o’i

Gwamnatin Jihar Borno ta taikaita bikin zagayowar Ranar Samun ’Yancin Kai Najeriya na bana zuwa addu’o’i, sakamakon mummunan ambaliyar ruwa a birnin Maiduguri da kananan hukumomin da ke kewaye.

Kwamishinan Yada Labarai da Tsaro na jihan, Farfesa Usman Tar, a cikin wata sanarwa Litinin, ya jaddada bukatar zurfafa tunani tare da hadin kai a wannan lokaci na jarabawa a jihar.

Ambaliyar, wadda ta shanye sama da kashi 70 na garin Maidugrui ta yi mummunar barna, inda da ta shafi daruruwan iyalai tare da lalata muhimman ababen more rayuwa kamar asibitoci da makarantu da hanyoyi da gadoji da sauransu.

Kwamishinan ya ambato Gwamna Babagana Zulum yana sake nuna tausayawarsa ga duk wadanda abin ya shafa tare da yin kira ga al’ummar Borno su hada kai wajen yi wa jihar da kasa baki daya addu’a.

“A yayin da ranar ’yancin kan kasarmu ya zagayo, dole ne mu mayar da hankali wajen tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta ranar 10 ga Satumba ta shafa.

“Mu yi amfani da wannan lokacin wajen yin addu’ar farfadowa da samun karfin gwiwa a jihar Borno da ma da Najeriya baki daya.

“Gwamnati za ta dukufa wajen gyara ababen more rayuwa da ambaliyar ta lalata da samar da agaji tare da tabbatar da cewa iyalan da abin ya shafa sun sami tallafin da ya dace,” in ji sanarwar.

Gwamnan ya tabbatar wa al’ummar Borno cewa gwamnatinsa na aiki da kwamitin rabon kudaden tallafi domin gaggauta isar kayan agaji yadda ya kamata ga jama’ar.

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro