Ranar ’yanci kai ko ta kwatar kai?
A shekaranjiya Laraba kasar nan ta cika shekaru 54, cif-cif da samun `yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya, wato 1 ga watan Oktoban 1960, bayan sun hade Arewaci da Kudanci a cikin shekarar 1914, don su samu saukin gudanar da mulkin yankunan biyu. kasar nan dai ita ce kasa ta uku daga […]
A shekaranjiya Laraba kasar nan ta cika shekaru 54, cif-cif da samun `yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya, wato 1 ga watan Oktoban 1960, bayan sun hade Arewaci da Kudanci a cikin shekarar 1914, don su samu saukin gudanar da mulkin yankunan biyu. kasar nan dai ita ce kasa ta uku daga cikin kasashen Nahiyar Afirka da suka samu `yanci kai daga Turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya. kasar Ghana da ada ake kira Gold Coast ita ta fara samun `yancin kai ranar 06-03-1957, sannan sai kasar Somaliya ranar 01-07-1960. Babu ko shakka a irin wannan rana akwai bukatar a yi waiwaye adon tafiya akan irin tsawon tafiyar da aka ratso da sunan kasa mai yancin kai, sannan kuma a yi godiya ga Allah SWT, bisa ga da dadi, ba dadi, har yanzu dai muna zaune da sunan kasa daya, duk da kalubalen zamantakewar da kullum take ta kara tabarbArewa.
Jam`iyyun siyasa na jamnhuriyar farko da suka karbi `yancin kai daga hannun `yan mulkin mallaka, irin su NPC, ta Firimiyan jihar Arewa na farko kuma na karshe, Alhaji Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakwwato, duk da ita ta fara kafa gamnatin tsakiya, amma har ta yi zamaninta ta gama a shekarar 1966 (da sojoji suka fara juyin mulkin farko), ba ta taba cin zabe ba a Kudanci da gabashin kasar nan. Haka ita ma jam`iyyar AG ta Cif Obafemi Awolowo, Firimiyan Jihar Yamma, ita ma ba ta taba cin zabe a Arewa ba, bare a gabashin. Ita kanta jam`iyyar NCNC ta Dokta Nnamdi Azikwe, da suka yi kawance da jam`iyyar NPC har suka kafa gwamnatin tsakiya, ba ta da tarihin a karan kanta ta taba cin zabe a Arewa bare a Yammacin kasar nan.
Hatta juyin mulkin sojan farko da aka fara yi a kasar nan ranar 15-01-1966, wanda a ciki aka kashe mnyan mutanen Arewa, irinsu Alhaji Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da Firayim Minista Sa Abubkar Tafawa Balewa da makamantansu `yan kabilar Ibo a karkashin jagorancin Manjo Chukwuma Kaduna Nzegwu suka shugabancesa, har suka nada dansu Manjo Janar J. T. U. Aguiyi-Ironsi, ya jagoraci mulkin kasar nan, na kusan watanni shidda, lokacin da `yan Arewa suka sake wani juyin mulkin a karo na biyu, cikin watan Yulin 1967, su kuma sukadora Laftanar Yakuba Gowon dan Arewa akan karagar mulkin.
Mai karatu, duk da wannan tubalin kabilanci da aka kafa wannan kasa yabon gwani ya zama dole don kuwa har gbe ba sai yu ba tarihi na tabbatar da cewa shugabannin farko sun yi iyakacin bakin kokarinsu, musamman na Arewa da suke da karancin ilmi, wajen aza kyakykyawan harsashin gina lardunansu da mutanensu, duk da yake tun kafin `yancin kan mutanen Kudancin kasar nan sun yi wa takwarorinsu na Arewa fintinkau akan batun fannin ilmin zamani, wanda har yanzu mutanen Arewar suke koma baya, duk kuwa da kasancewar da Bature ya zo ya taras da Arewa a cikin tsarin mulkin gargajiya, mai tsarin tafiyarwa akan koyowar addinin islama, wannan ya sanya Turawan suka ka ci gaba da mulkin Arewa ta karkashin tsarin Sarakunan, tsarin da aka rika kira “Indirect Rule,” yayin da a Kudanci su da kansu kai tsaye suka rinka tafiyar da mulkinwato Direct Rule.
Koda wai ba aniyar wannan makala ba ce ta yi tsokaci akan ba a samu ci gaba a cikin wadannan shekaru ba, don kuwa koda a kasa babu gamsuwa akan irin yadda shugabannin da suka biyo bayan shugabannin farko cikin iya ririta dukiyar jama`a cikin kamanta gaskiya da rikon amana, amma ga `yan kasa da garuruwansu kasancewa akwai inda aka samu ci gaba koda kuwa na mai hakar rijiya ne. Sau tari ni kan ce “Mu mutanen wannan zamanin muna cikin wadatar dukiya da ilmi (na zamani da na addini), da Iyayenmu da Kakanninmu ba su taba mafarkin al`ummar da za ta biyo bayansu, Allah zai azurta su da su ba” Amma ba nan gizo yake sakar ba, su magabatanmu sun rayu cikin taimaka wa juna da kamanta gaskiya da adalci cikin dukkan harkokinsu na yau da kullum kuma koda da wa za su yi mu`amala, ba tare da la`akari da komai ba, sai don kawai sun yi imani da cewa haka Allah Ya ce su yi.
Yanzu dauki kasashen duniya irin su Brazil da Indiya da Malesiya da Indunisiya, wadanda a shekarun 1960, tare muka fara rarrafen mu tashi, akan fannonin rayuwa daban-daban, kamar iya ciyar da kai abinci da fannin kimiyya da fasahar kere-kere ko samar da wutar lantarki da ayyukan yi da ilmi da makamantan ayyukan raya kasa. Wadannan ci gaba da kasashen suka samu, sun samu ne bisa iya tsayawarsu akan kamanta gaskiya da adalci da kishin kasa da suka gada daga shugabanninsu na farko da suka karbi mulkin kasashensu daga `yan mulkin mallaka, sabanin mu da muka barar da ayyukan alherin magabatanmu na farko, duk kuwa da dimbin arzikin ayyukan noma da kiyo da na man fetur da Allah Ya ba mu daga baya.
Yanzu ma duk ba wannan ba, rikicin `yan kungiyar Jama`tu Ahlis Sunnah Lid Da`awati Wal jihad da ake kira Boko Haram da muke ciki, yau sama da shekaru hudu, shi kadai ya ishe mu tashin hankali, don kuwa ko da yakin basasar watanni 30, da muka yi tsakanin shekarar 1967 zuwa farkon 1970 bai jefa mutanen kasar nan cikin tabarbarewar rayuwa irin ta wannan karon ba, tabarbarewar da ta kai fagen kowa ka gani mai mulki da talaka; mai shi da marasshi a rude ake, koda kuwa inda ba rikicin bai kai ba, a inda kuwa ake rikicin sai addu`a, don kuwa a karon farko Sarakuna na guje wa fadarsu, suna tafiya gudun hijira, baya ga dubban manya da kananan mutanen da aka kashewa da wadanda aka jikkata da miliyoyin da bayan an kona garuruwansu yanzu sun zama `yan gudun Hijjira a cikin kasarsu da kasashen makwabta, irinsu Chadi da Kamaru da Jamnhuriyar Nijar.
Haka duk na faruwa ne a bisa ga rashin mulkin kamanta gaskiya da adalci daga shugabanni da kuma rashin kyautatawa tsakanin junanmu ta kowane fanni.
Ina ganin lallai daga wannan rana ya kamata mu yi kudurin ganin mun kwaci kanmu, ta hanyar kamanta gaskiya da adalci cikin dukkan mu`amalolinmu, tsakaninmu da Mahaliccinmu da iyalinmu da `yan uwanmu da makwabtanmu da sauran abokan zamanmu, ba tare da nuna bambancin addini ko jinshi ko yare ba. kudurta haka da aiwatarwa za su sa da yardar Allah a zabubbukan shekara mai zuwa Allah zai yi mana jagora, mu zabi shugabanni na gari da za su fitar da mu kuncin rayuwar da mafi yawan `yan kasa muke ci. Barka da zagayowar ranar `yancin kai Allah maimaitamana cikin rahamarSa.