Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta 2016

A ranar 3 ga watan Mayun kowace shekara ce ake yin bikin zagayowar ranar ’yan jarida a dukkan fadin duniya.  Rana ce da ’yan jarida ke janyo hankalin duniya don sanin muhimmancin ’yancin ‘yan jarida.  Haka kuma rana ce da ’yan jaridu ke tuna takwarorinsu da aka kashe yayin da suke gudanar da ayyukansu na […]

Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta 2016
Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta 2016

A ranar 3 ga watan Mayun kowace shekara ce ake yin bikin zagayowar ranar ’yan jarida a dukkan fadin duniya.  Rana ce da ’yan jarida ke janyo hankalin duniya don sanin muhimmancin ’yancin ‘yan jarida.  Haka kuma rana ce da ’yan jaridu ke tuna takwarorinsu da aka kashe yayin da suke gudanar da ayyukansu na watsa labarai.  Bikin ranar ta wannan shekara (2016) ta yi daidai da muhimman abubuwa uku ga ’yan jaridu a wannan shekara.  Da farko yau (2016) kimanin shekara 250 kenan da kafa dokar sakarwa ’yan jarida mara a kasashen Sweden da Finland.   Sannan wannan shekara ta zo daidai da dokar ’yancin ’yan jarida da aka yi yau kimanin shekara 25 a Windhock.  Haka kuma wannan shekara ta kasance ita ce ta farko daga cikin shekaru 15 da aka kayyade don ganin an cimma burin bunkasa tattalin arziki a sassan duniya (Sustainable Development Goals, SDGs).
Don haka bikin ranar ’yancin ’yan jarida ta bana ta yi tsokaci ne a kan sakar wa ’yan jarida mara wajen yin aikinsu da kuma ba su kariya a lokacin da suke gudanar da ayyukansu da kuma sanin yadda tattalin arzikin kasa ke tafiya.
A duk duniya, wannan bikin na ranar ’yancin ’yan jarida ya mayar da hankali ne akan muhimman batutuwa uku, watau ’yancin samar da bayanai da na kare ’yancin ’yan jarida da kuma tabbatar da ana ba su kariya a duk inde suke gudanar da ayyukansu.
An wayi gari a yau ana take hakkin ’yan jarida ba tare da ana shakka ba.  An san ’yan jarida wajen sadaukar da rai da jajircewa wajen kwato wa marasa karfi hakki.
A Najeriya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a wani sako da ya aika a ranar ’yan jaridu ta 2015 jim kadan bayan ya zama shugaban kasa ya nuna gwamnatinsa tana mutunta ’yan jarida don haka ba ta tauye hakkin kowane dan jarida a kasar nan.
Ya bayyana haka ne ta bakin Ministan watsa labarai Alhaji Lai Mohammed a taron ’yan jaridun Afirka da ya gudana a Abuja.  Ministan ya ce:  “Gwamnatin Buhari ba ta taba tsangwama ko cin mutuncin wani dan jarida ba musamman a lokacin da yake gudanar da aikinsa ballantana ta yi tunanin kashe shi.  Don haka ina sanar da wannan taro cewa babu wani dan jarida da gwamnatin Najeriya ta tsangwama ko ta kashe a lokacin da yake gudanar da aikinsa, wannan gwamnati ta kowa ce kuma tana ba kowane dan kasa hakkinsa daidai gwargwado”.
Sai dai kungiyar kare hakkin ’yan jarida ta ce ta yarda da kalaman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na rashin tsangwamar ’yan jarida wadansu abubuwa marasa dadi da suka faru da ’yan jarida daban-daban daga bara kawo yanzu sun zama abin dubawa da kuma yin takaici.
Duk da wannan ikikari na Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a watan Yunin bara (2015) an samu labarin yadda wadansu ’yan sanda suka ci mutuncin wani dan jaridar da ke aiki da Gidan Rediyon Tarayya mai suna Muhammad Atta-Kafin-Dangi  a lokacin da yake yunkurin daukar rahoton zanga-zangar wadansu ’yan acaba a Jihar Nasarawa.   Baya ga wannan an sake samun labarin yadda wadansu jami’an Hukumar Kwastam suka yi wa  mai mujallar Prime Magazine Yomi Omolofe dukan kawo wuka a Badagry da ke Jihar Legas a kokarin da ya yi na bincikar labarin yadda ake hada baki da wadansu daga cikin jami’an hukumar da ’yan sumoga a iyakar Najeriya da Benin. An ce kimanin jami’an hukumar su kimanin 15 ne suka yi masa dirar mikiya a lokacin da ya ziyarci ofishinsu don neman karin bayani.
Haka kuma a watan Nuwamban bara (2015) an sake samun labarin yadda wadansu daga cikin jami’an hukumar gidan yari (Nigerian Prison Service) da wadansu mutane suka yi wa wakilin jaridar banguard Emmanuel Elebeke dirar mikiya a lokacin da yake kokarin daukar hoton wadansu mutane uku da ake zargi da laifin kisan kai  a harbar Kotun daukaka kara da ke Abuja.  Sannan a watan Fabrairun wannan shekara (2016) ne aka samu rahoton yadda Jami’an Hukumar da’ar Mutane (Nigerian Civil Defence Corps) suka kama wadansu ’yan jarida uku a garin Owerri na Jihar Imo a lokacin da suke gudanar da ayyukansu.
Wadannan abubuwa da suka faru sun nuna akwai bukatar gwamnatin Buhari ta sanya ido don ganin ba su cigaba da faruwa ga ’yan jaridu ba. Idan suka ci gaba da faruwa ba tare da gwamnatin ta dauki mataki ba, to zai zama kalaman da ya yi na kare ’yancin ’yan jaridu sun zama tamkar shaci-fadi.
 Abu mafi muhimmanci a yau shi ne yakamata ’yan jarida su san muhimmancin bayar da sahihan labarai wadanda ba shaci-fadi wadanda za su iya tayar da hargitsi a kasa ba.   Saboda haka ya dace masu gidajen yada labarai su rika wayar da kan ma’aikatansu a kan muhimmancin watsa sahihan labaran da suka tantance da kuma wadanda za su hada kan kasa.  Sai dai za a samu nasarar haka ne kawai idan aka rika biyan ’yan jarida albashi da wadansu hakkokinsu a kan lokaci.
Akwai bukatar gwamnati ta rika mutunta aikin ’yan jarida ta hanyar ba su dama wajen gudanar da ayyukansu ba tare da yin katsalanda, tsangwama ko cin fuska ba.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu