‘Ranar Yara Mata: An koyar da mu a Najeriya daidai da ’ya’yan turawa’

A zamanin da an fi daukar ’ya’ya mata da daraja kuma duk yarinyar da ta kammala sakandare, tana da kwarewar yin kowane irin aikin ofis

‘Ranar Yara Mata: An koyar da mu a Najeriya daidai da ’ya’yan turawa’

Tsohuwar Ministar Harkokin Mata, A’isha Isma’il, ta ce nagartar ilimin da ake bayarwa a makarantun gwamnati a Najeriya a zamaninsu daidai yake da wanda ake bai wa ’ya’yan turawa a kasar Birtaniya.

Ta ce a zamaninsu an fi daukar ’ya’ya mata da daraja kuma duk yarinyar da ta kammala makarantar sakandare, to tana da kwarewar da za ta iya gudanar da kowane irin aikin ofis a kowane mataki.

A hirarta da Aminiya albarkacin Ranar ’Ya’ya Mata ta Duniya ta 2022, Hajiya A’isha ta fayyace bambancin tarbiyyar ’ya mace da na da namiji da matsalolin kowannensu.

Ta kuma bayyana abin da ya lalata harkar ilimi a Najeriya da kuma hanyoyin da za a bi domin shawo kan matsalar.

Sojoji sun kama masu ƙera makamai a Kebbi

Bam ya kashe aƙalla mutum shidda a Siriya

’Yan bindiga sun kashe Limami da wasu a Sakkwato

Gwamnati za ta mayar da yara 5,000 makaranta a Jigawa

Tags