Ranar yara: Waje 6 da ya kamata yara su ziyarta don shakatawa
Akwai wasu wurare shida a Legas, Abuja da Kano da za a iya zuwa don yin nishadi.
Najeriya ta ware ranar 27 ga wane watan Mayun kowace shekara a matsayin Ranar Yara, wanda ya sa ta kasance rana mai muhimmanci ga iyaye da su kansu yaran.
Yara na daya daga cikin ni’imar da ubangiji ke bai wa iyaye, don haka yana da kyau a ce sun mori wannan rana tasu ta musamman da aka ware domin su.
- Uba Sani ya samu tikitin takarar Gwamnan APC a Kaduna
- Ya kamata a yi dokar da za ta hana raba wa daliget kudi —Jonathan
Da akwai wasu wuraren nishadi guda shida da Aminiya ta yi nazari, wanda za su ba da ma’ana idan aka kai yara don yin nishadi a Legas, Abuja da kuma Jihar Kano:
1. Wurin shakatawa na Hi-Impact Planet
Wannan wani waje ne na wasanni da aka bude a Jihar Legas. Kuma yana dauke da kayan wasanni na yara da manya na zamani da mutum zai iya amfani da su don yin nishadi musamman a lokacin da ya ke bukatar debe kewa.
Wurin na yankin Ibafo kan hanyar babban titin Legas zuwa Ibadan. An bude wurin nishadin a watan Disamban 2015.
2. Wurin shakatawa Frankids
Wannan waje yana daya daga cikin wuraren nishadi mafi kyau da kayatarwa a Jihar Legas. Wuri ne da ke dauke da kayan wasanni da nishadi na musamman.
Wurin yana yankin FESTAC a unguwar Badagry da ke Jihar Legas.
3. City Park
Idan kuwa ana maganar wurin nishadi da shakawa a Babban Birnin Tarayya Abuja, to dole ne a saka ‘City Park’ a matsayin wuri na gaba-gaba saboda tsananin kyau da tsari da ya ke da shi.
Wuri ne da ya hada kayan wasa, motsa jiki, nishadi sa sauransu, kazalika ana sayar da kayayyakin makulashe.
Wurin yana nan a lamba 136 titin Ademola Adetokunbo, a Wuse 2, Abuja.
4. Wurin shakatawa na Durumi
Durumi yana da kayan nishadi da wasa na yara na musamman. Idan ana maganar samun sauki da kuma biyan bukata wajen yin nishadi, to wurin wasan yara na Durumi ya ciri tuta.
Har wa yau, wuri je da ke tsaro na musamman, yana kan titin Oladipupo Diya St, Durumi, a Abuja.
5. Gidan Zoo
Gandun adana dabobbi na Jihar Kano, wato (Gidan Zoo) wuri ne ake debe kewa da yin nishadi kama daga yara har zuwa manya.
Wuri ne da ke dauke da nau’in dabobbi daban-daban, kama daga Zaki, Kura, Giwa, Damisa da sauransu.
Wurin na kan titin ‘Zoo Road’ a Kano.
6. Gidan Makama
Idan kuwa maganar kayan tarihi ake yi, idan aka ambaci Gidan Makama a Jihar Kano magana ta kare.
Mutum na iya daukar iyalinsa, don zuwa Gidan Makama baje kolin kallon kayan tarihi.
Kuma ziyarar wannan gida za ta bada ma’ana musamman ga yara kananan a wannan lokaci da ake bikin ranarsu ta duniya.
Gidan na nan daura da Gidan Sarkin Kano, a cikin kwaryar birnin Kano.