Ranbo ya karyata batun jita-jitar mutuwarsa
Fitaccen jarumin fina-finan Hollywood Sylbester Stallone wanda aka fi sani da Ranbo ya karyata batun jita-jitar ya mutu a hadarin mota.A ranar Asabar ne aka yada batun mutuwar jarumin a shafin facebook, inda aka ce ya mutu sakamakon mummunan hadarin mota.Sanarwar a shafin facebook ta ce: “Da misalin karfe 11 na safiyar Asabar (13 ga […]
Fitaccen jarumin fina-finan Hollywood Sylbester Stallone wanda aka fi sani da Ranbo ya karyata batun jita-jitar ya mutu a hadarin mota.
A ranar Asabar ne aka yada batun mutuwar jarumin a shafin facebook, inda aka ce ya mutu sakamakon mummunan hadarin mota.
Sanarwar a shafin facebook ta ce: “Da misalin karfe 11 na safiyar Asabar (13 ga Satumba, 2014) jarumi Sylbester Stallone ya mutu. An haifi jarumi Sylbester Stallone a ranar 6 ga Yuli, 1946 a Birnin New York da ke Amurka. Ba za a taba mantawa da shi ba, don haka ku mika sakon ta’aziyyarku ta hanyar yada wannan labarin.”
Hakan ya sanya dubban jama’a suka rika yada labarin mutuwar jarumin mai kimanin shekara 68.
A ranar Lahadi ne jarumin ya karyata batun jita-jitar inda mai magana da yawunsa ya ce jarumin na cikin koshin lafiya.
Ya ce: “Jarumin na cikin koshin lafiya, don haka kada a rika yarda da duk wani labari da aka gani a intanet.”