Rarara da mawakan 13×13 sun yi waka kan matsalar tsaro
Mawakan dai na kiran gwamnati da ta kara azama a kan sha’anin tsaro
Fitaccen mawakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Jam’iyyar APC, Dauda Kahutu Rarara da sauran mawakn kungiyar da yake shugabanta ta 13×13, sun yi waka domin kira ga gwamnati da ta yi wani abu kan rashin zaman lafiya a Najeriya.
A cikin wakar mai taken ‘Kasata ita ce gaba’ Aminiya ta jiyo Rarara yana cewa “kasata ita ce a gaba, gwamnati ki fito ki kara himma a sha’anin tsaro, sai da tsaro arkizin kasa yake kara cigaba.”
- Kane Tanaka: Tsohuwar da ta fi kowa yawan shekaru a duniya ta rasu
- Mutum 200 sun mutu a wani sabon rikici a Sudan
Ya kara da cewa, “Yanzu fa jama’ar gari kadan ke muku uzuri, dan ko yanzu abin ya yawaita kauye har gari.”
A nasa baitocin, Ali Jita ya ce babu duk laifin gwamnati ne, domin ita ce ke da hakkin kare rayukan mutane.
Daga cikin mawakan da suka yi wakar akwai Dauda Kahutu Rarara da Nura M. Inuwa da Umar Shareef da Aminu Ala da Ali Jita da Baban Chinedu da Adam A. Zango da sauransu.
Akwai jarumai irinsu Yakubu Mohammed da Aishatu Humaira da Abale da sauransu.
Abubakar Bashir Maishadda ne ya shirya, sannan Ali Gumzak da Aminu S. Bono da Mustapha Shareef da Hassan Giggs da Saifullahi Safzor da Oly Play Msk suka ba da umarni.