Rarara: Ina wakar Buhari da ’yan Najeriya suka biya kudade?
Wasu na zargin mawakin ya yi sama da fadi da kudaden mutane da ya amshe
Watanni biyar bayan amsar kudaden ’yan Najeriya da mawaki Dauda Kahutu Rarara ya yi, har yanzu ya gaza yin wakar Shugaba Buhari da ya yi alkawari.
A watan Satumbar 2020 ne Rarara ya bukaci masoya Buhari su ba da tallafin N1000 don ya buga wa Buhari sabuwar wakar da za ta daga darajarsa a duniya.
- Ba’amurkiyar da ta kashe dan Najeriya ta shiga hannu
- ’Yan sanda sun yi wa ’yan bindiga luguden wuta a Zamfara
- Duk wanda aka gani da bindiga a kamo shi —Buhari
- ’Yan sanda sun yi wa ’yan bindiga luguden wuta a Zamfara
- Tsohon Sarkin Kano ya magantu kan dakatarwar da aka yi wa Sheikh Abduljabbar
A lokacin, Rarara ya ce, “Ina so na karyata masu cewa farin jinin Buhari ya dusashe a zukatan talakawa.
“Kowa ya san Buhari na talakawan Najeriya ne, don haka nake kiran magoya bayan Shugaban Kasa da su ba da N1000 don buga masa sabuwar waka.
“Wannan ba komai ba ne face farfaganda daga makiya wai talakawa sun daina son Buhari.
“Idan har suka ba da kudin da aka yi wa Buhari waka, hakan ya nuna har yanzu talakawa na tare da shi.”
Sai dai mutane da dama na tambayar shin mawakin bai samu isassun kudin da za a buga wa Buhari wakar ba ne, ko kuma wata hanya ce da zai yi wa talakawa zamba?
Tun daga wancan lokaci an yi ta kokarin jin ta bakin mawakin kan lamari amma haka ba ta cimma ruwa ba, saboda an gaza samun sa a waya.
Kazalika, wasu sun bayyana rashin jin dadinsu kan yadda mawakin ya gaza buga wakar tare da rashin bayyana adadin kudaden da aka tara kamar yadda ya yi alkawarin bayyanawa tun farko.