Rarara ya gwangwaje ’yan Kannywood 57 da kyautar 50,000 kowannensu
Mawakin ya raba tallafin don taimakon ’yan masana’antar shirya fina-finan ta Kannywood
Fitaccen mawakin wakokin siyasar Kannywood, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ya gwangwaje ’yan Kannywood mutum 57 da kyautar kudi N50,000 kowannensu.
Hadimin mawakin kan kafafen watsa labarai, Rabiu Garba Gaya ne ya bayyana haka, inda ya ce tallafin na ciki ire-iren ayyukan kungiyar 13×13, wadda Rarara ke jagoranta.
- Laifukan yaki: MDD ta bukaci Rasha ta mika wuya ga kotun ICC
- Wani Bature ya harbe bakar fata kan zargin dorinar ruwa ce
A cikin sanarwa da ya sanya wa hannu, ya ce an bai wa jarumai iyaye mata 13 da jarumai iyaye maza 15 kyautar 50,000 kowannensu.
Sannan ya ce Rarara ya bai wa jarumai mata 10 kowanensu kyautar 50,000, yayin da kuma mawaka mata masu aure suka samu kyautar 30,000 kowannensu.
Tuni wadanda suka ci gajiyar tallafin suka shiga bayyana godiyarsu ga mawakin a shafukansu na sada zumunta.
Sabuwar tafiyar 13×13 wadda Rarara ke jagoranta ta kunshi jarumai, mawaka, furodusoshi da daraktoci daga masana’antar shirya fina-finan Kannywood a matsayin ’ya’yan kungiyar.
Idan ba a manta ba a baya-bayan nan mambobin 13×13 suka dawo daga birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) inda suka je yawon shakatawa da kungiyar ta dauki nauyi.