Hotuna: Rarara ya yi hatsarin mota

Shugaban kungiyar ’yan Kannywood na 13X13, Dauda Adamu Abdullahi (Rarara) ya yi hatsarin mota

Hotuna: Rarara ya yi hatsarin mota

Fitaccen mawakin siyasa kuma shugaban kungiyar ’yan Kannywood na 13X13, Dauda Adamu Abdullahi (Rarara) ya yi hatsarin mota.

Mai magana da yawun mawakin, Rabiu Garba Gaya ne ya sanar a safiyar Juma’a cewa Rarara ya yi hatsarin ne a hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama, amma bai bayyana ko a ina ba ne.

A sanarwar da ya fitar ta shafinsa na Facebook, hadimin a Raraya ya dora hotunan yada motar mawakin ta fada a cikin wata katuwar lambatu da kuma yadda gaban motar ya yi kaca-kaca.

Sai dai ya bayyana cewa,  duk da hatsarin, Raraya yana cikin koshin lafiya.

Ga hotunan hatsarin da hadimin nasa ya fitar:

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu