Rasha da Isra’ila na zaman tsama a kan rikicin Syria
kasar Rasha ta bayyana matakin da Isra’ila ta dauka dangane da harbo wani jirgin yakin kasar a matsayin abin alhini da kuma abin kyama. Rashar ta kuma yi tir da matakan da sojojin sama na Isra’ila suka dauka, wadanda kuma take ganin su ne dalilin harbo daya daga cikin jiragenta na yaki a Syria. Ta […]

kasar Rasha ta bayyana matakin da Isra’ila ta dauka dangane da harbo wani jirgin yakin kasar a matsayin abin alhini da kuma abin kyama.
Rashar ta kuma yi tir da matakan da sojojin sama na Isra’ila suka dauka, wadanda kuma take ganin su ne dalilin harbo daya daga cikin jiragenta na yaki a Syria.
Ta bayyana cewa a bayyane yake cewa Isra’ila na daukar wasu matakai domin yin kafar ungulu ga tsarin zaman lafiyar da ke samuwa a kasar.
kasar Isra’ila ta musanta cewa tana da hannu a wannan lamarin da ya auku.
Girman matsalar ta sa Rasha ta kira Jakadan Isra’ila zuwa Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar domin ta bayyana masa bacin ranta a kan asarar rayukan sojojinta da ke cikin wannan jirgi.
Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei bershinin ya gana da Mataimakin Jakadan Isra’ila, Keren Cohen Gat, a birnin Moskow.
Ya sanar da Jakadan na Isra’ila cewa Rasha ta yi tir da halayyar matuka jiragen yaki na rundunar sojojin Isra’ila, wadanda ta ce su ne suka janyo aka kakkabo jirgin yakin Rasha samfurin Ilyushin-20.
Dukan sojojin Rasha 15 da ke cikin jirgin sun rasa rayukansu kamar yadda BBC ya ruwaito.
Duk da cewa dakarun Syria ne suka harbo jirgin na Rasha, amma Rasha ta yi imanin cewa Isra’ila na da hannu dumu-dumu a kan lamarin.
Sanarwar Ma’aikatar Tsaro ta Rashar ta bayyana cewa Rasha za ta ci gaba da daukar dukan matakan da za su kare muradunta a yankin Gabas ta Tsakiya.