Rasha da Ukraine na kulla yarjejeniyar fitar da hatsi kasuwar duniya

Mamayar Rasha da ta datse tashoshin jiragen ruwan Ukraine ta haddasa tashin gwauron zabon hatsi tare da barazanar kawo karancin abinci a duniya.

Rasha da Ukraine na kulla yarjejeniyar fitar da hatsi kasuwar duniya

Hatsi

Kasar Rasha na dab da sanya hannu kan yarjejeniyar barin makwabciyarta Ukraine ta fara fitar da hatsi zuwa kasuwannin duniya.

A ranar Juma’a makwantan biyu ke rattaba hannu kan yarjejeniyar bayan gwamnatin kasar Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya sun jagoranci tattaunawar sulhun.

Matakin zai ba da damar bude tashoshin jiragen ruwan Ukraine domin fitar da hatsi zuwa kasuwannin duniya.

Mamayar Rasha da ta datse tashoshin jiragen ruwan kasar tun a watan Fabrairu ta haddasa tashin gwauron zabon hatsi da ke barazanar kawo karancin abinci a kasashen duniya.

Wannan dai ita ce babbar yarjejeniya ta farko da kasashen biyu da ke yaki da juna ke kullawa.

Yarjejeniyar na ba da kwarin gwiwar cewa barazanar karancin abincin da ake fuskanta za ta kau.

Me yarjejeniya ta kunsa?

Wani hadimin Shugaban Kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya ce ranar Juma’a za a sanya hannu kan yarjejeniyar a birnin Santanbul, babban birnin kasuwancin kasar.

Kawo yanzu dai ba a fitar da cikakken bayanin abin da ke kunshe cikin yarjejeniyar da Erdogan da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, suka shafe watanni suna neman ganin ta tabbata.

Amma wasu rahotanni na cewa makwabtan biyu sun amince za a binciki jiragen ruwan da za su shiga Ukraine da domin tabbatar da ba su dauko makamai da sauran kayan aikin soji.

Haka kuma za a binciki jiragen ruwan da suka taso daga tashoshin jiragen ruwan Ukraine zuwa wasu wurarare ta zirin Bosphorus.

Za kuma a kafa cibiyar lura da cika yarjejeniyar a Santanbul, kuma jami’an cibiyar za su fito ne daga gwamnatin Trukiyya, Majalisar Dinkin Duniya, Rasha da kuma Ukraine.

Ukraine ta kuma bukaci Rash ba za a yi amfani da damar ba wajen kai hari a tashar jirgin ruwa da ke Odessa.

Kawo yanzu dai Rasha da Ukarine ba su tabbatar da yarjejeniyar ba, amma a wani bidiyo da ya fitar ranar Alhamis da dare, Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy  ya nuna nan ba da jimawa ba za a bude yankin.

A ranar Alhamis da dare Guterres ya isa birnin Santanbul da domin bikin sanya hann kan yarjejeniyar washegari.

Amurka ta yi maraba da matakin, amma tana taka-tsantsan, tare da cewa ta dora wa Rasha alhakin kiyaye yarjejeniyar.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos