Rasha da Ukraine sun amince da shirin musayar fursunoni
Mun amince da musayar fiye da fursunoni 40 daga kowane bangare.
Rasha da Ukraine sun amince da wani sabon shirin musayar fursunoni a tattaunawar da suka yi a taron kasa da kasa da ke gudana a Turkiyya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa AFP ya ruwaito cewa, tattaunawar da ba kasafai ake yi ba ta kuma tabo batun samar da hanyar ayyukan jin kai a tsakanin kasashen biyu.
Jami’in kare hakkin bil’adama na Ukraine, Dmytro Lubinets ya gana da takwararsa ta Rasha Tatyana Moskalkova a gefen taron kasa da kasa da ake yi a birnin Ankara wanda Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya halarta.
Moskalkova ta shaida wa manema labarai bayan taron cewa, sun amince da musayar fiye da fursunoni 40 daga kowane bangare.
Sai dai Mr Lubinets na Ukraine bai ambaci wani adadi ba a cikin jawabinsa ga manema labarai bayan tattaunawar sa’o’i uku.
“Ba mu gama tattaunawar ba. Za mu ci gaba,” inji shi.
Ana sa ran jami’an kare hakkin bil’adaman biyu za su yi musayar jerin sunayen fursunonin da duk wata yarjejeniyar da za a yi, a wani taron a wannan Alhamis din.
Jami’in kare hakkin bil’adama na Turkiyya Seref Malkoc ya taimaka wajen shiga tsakani a taron na ranar Laraba.
“Jami’an biyu sun bayyana wata bukata ta bai daya — don bude hanyar jin kai karkashin kulawar Recep Tayyip Erdogan, kamar yadda aka kulla yarjejeniyar fitar da hatsi,” in ji Malkoc.
Daga baya Erdogan ya shaida wa taron kasa da kasa cewa “a shirye” ya ke ya sa ido kan hanyar kula da masu bukatar jin kai.
Wannan matakin dai na zuwa ne duk da fadan da ya barke a tsakanin Rashar da Ukraine tsawon watanni 11 da suka gabata.