Rasha na ci gaba da tsananta kai hare-hare a Ukraine
Fiye da mutum dubu dari takwas sun tsere daga Ukraine zuwa yanzu.
Rasha na ci gaba da tsananta kai hare-hare kan tashar jirgin ruwa da ke Mariupol inda hukumomi suka ce akwai yiwuwar an halaka daruruwan mutane.
Mataimakin magajin garin ya shaida wa BBC cewa ruwan makaman da Rasha take ta yi, ya lalata kusan baki dayan wata gunduma, wadda take da mutane sama da dubu 100.
- MDD ta yi Allah wadai da mamayar Rasha a Ukraine
- Ya kamata Ronaldo da Messi su hakura da kwallo haka —Platini
Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutum dubu dari takwas sun tsere daga Ukraine zuwa yanzu.
Ministocin cikin gida na Turai na gab da fara tattaunawa kan wata shawara da hukumar Turai ta gabatar ta neman a bai wa mutanen da ke tserewa yaki a Ukraine kariya ta wuccin gadi.
BBC ya ruwaito cewa haka suma biranen Chernihiv da Kharkiv da ke arewacin kasar sun sha mummunan harin makaman atilari na Rasha.
Rasha dai ta tsananta hare-harenta a kan muhimman wurare a fadin kasar ta Ukraine, inda hukumomin bayar da agajin gaggawa suka yi kiyasin cewa sama da mutum 2000aka kashe tun da aka fara mamayar.
Can kuma a wani bangaren yayin da wata babbar kwamba ta dakarun Rasha ta durfafi, Kyiv, mazauna garin Ivankiv, da ke arewa da babban birnin sun ce sun kasa tserewa, bayan da sojin na Rasha suka kame iko da yankin a makon da ya wuce.