Rasha ta ba da umarnin kammala gyaran gadar Crimea a wata 7

Fira Minista Mikhail Mishustin ya bayar da umarnin kammala gyaran gadar da ta hada kasar da yankin Crimea kafin watan Yuli na 2023.

Rasha ta ba da umarnin kammala gyaran gadar Crimea a wata 7

Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin

Gwamnatin Rasha ta bayar da umarnin kammala gyarna gadar saman da aka kai wa hari a bom a karshen mako cikin wata bakwai.

Fira Minista Mikhail Mishustin ya bayar da umarni a safiyar Juma’a na kammala aikin gyaran gadar da ta hada kasar da yankin Crimea kafin ranar 1 watan Yuli na 2023.

A ranar Asabar ne aka kai harin bom a gadar, wadda ke dauke da layin jirgin kasa da tituna, wadda kuma aka amfani da ita wajen dakon mai ta jirgin kasa daga Rasha zuwa Crimea.

Rasha ta yi zargin abokan gaba ne suka kai mata harin, wanda daga bisani ta tsananta kai munanan hare-hare kan makwabciyarta, kasar Ukraine da suke yaki.

Kimanin wata 10 ke nan da kasashen biyu ke yakar juna tun daga ranar 23 ga watan Disamban 2021.

Mamayar ta Rasha dai ta yi ajalin dubban mutane da baya ga asarar dukiyoyi da raunata mutane tare da tilasta wa dubban jama’ar Ukraine yin gudun hijira.

Kasashen duniya sun yi tir da harin an Rasha, inda suke bai wa Ukraine goyon baya da gudummawa.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos