Rasha ta ci gaba da isar da iskar gas zuwa Turai —Gazprom

AN ci gaba da isar da iskar gas saboda yadda mabukata ke kwararowa a nahiyar Turai.

Rasha ta ci gaba da isar da iskar gas zuwa Turai —Gazprom

Gazprom

Kamfanin iskar gas na Rasha Gazprom ya ce ana ci gaba da isar da iskar gas na Rasha zuwa Turai.

Gazprom ya ce hakan na gudana ne duk da rikicin da ake na Ukraine da kuma takunkumin karya tattalin arziki da kasashen yammacin duniya suka kakaba wa Rashar.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito, kamfanin Gazprom a ranar Asabar ya ce sun ci gaba da aikin isar da gas din a nahiyar Turai laakari da karuwar masu bukatarsa.

Gazprom ya ce ya zuwa ranar 19 ga watan Maris, an bukaci iskar gas wadda nauyinta ya kai cubic meter miliyan 106.6 daga nahiyyar ta Turai.

Kamfanin ya ce farko lokacin da dakarun Rasha suka kai hari a Ukraine, an dan samu damuwa na ‘yan kwanaki na katsewar isar da iskan gaz din, amma daga baya kamfanin ya koma aikinsa.

Kamfanin na Gazprom ya ce a duk rana sama da murabba’in cubic miliyan 109 na iskan gaz din suke shigar da shi a nahiyar turai Turai ta hanyar Ukraine.