Rasha ta ci ribar Yuro Biliyan 98 a kwanaki 100 na yakinta da Ukraine

Duk da kasashen duniya sun juya mata baya, amma hakan bai hana ta samun kudaden shiga ba.

Rasha ta ci ribar Yuro Biliyan 98 a kwanaki 100 na yakinta da Ukraine

Shugaban Rasha, Vladmir Putin

Wani bincike ya bayyana cewar Rasha ta ci ribar Yuro biliyan 98 daga man da take sayarwa a kasashen duniya a cikin kwanaki 100 da aka kwashe ana yakin Ukraine, kuma akasarin man an kai shi kasashen Turai ne.

Rahotan binciken da Cibiyar Binciken makamashi ta CREA da ke Finland ta gudanar na zuwa ne a daidai lokacin da Ukraine ke kara kira ga kasashen Yammacin duniya da su kawo karshen duk wata cinakayyar da ke tsakanin su da Rasha domin hana ta samun kudade.

A farkon wannan watan, kungiyar kasashen Turai ta amince da shirin katse sayen mai daga Rasha wanda nahiyar ta dogara a kai, duk da yake kungiyar na shirin rage cinikin iskar gas na kashi biyu bisa uku kan yadda ta saba saye.

Rahotan binciken ya ce kasashen Turai sun sayi kashi 61 na man da Rasha ke fitarwa a cikin kwanaki 100 da aka kwashe ana yakin Ukraine wanda kudin sa ya kai yuro biliyan 57.

Kasar China ita ta fi sayen mai a Rasha da kudin sa ya kai yuro biliyan 12.6 sai kasar Jamus mai yuro biliyan 12.1 sannan Italiya mai yuro biliyan 7.8.

Rahotan binciken ya ce Rasha tafi samun kudin shigar ta daga bangaren man fetur da kudin sa ya kai yuro biliyan 46, sai iskar gas da kayayyakin da ake fitarwa daga albarkatun mai sannan gawayi.

Raguwar kasuwanci

Binciken ya ce kayayyakin da Rasha take fitarwa zuwa kasuwannin duniya sun ragu, sakamakon yadda kasashen duniya suka juya mata baya saboda mamayar Ukraine, amma hakan bai hana ta samun kudade ba saboda yadda farashin makamashin ya tashi a kasuwannin duniya.

Daga cikin kasashen da suka kara yawan makamashin da suke saya daga Rasha akwai China da Indiya da Daular Larabawa da kuma Faransa.