Rasha ta fara dibar sojojin haya a Afirka
Rasha dai na kokarin fadada tasirinta ne a Afirka
Kamfanin sojojin haya na kasar Rasha da aka fi sani da Wagner ya ce ya fara daukar dakarun da za su yi aiki da shi daga kasashen Afirka.
Shugaban kamfanin, Yevgeny Prigozhi ya wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna ma’aikatan kamfanin da aka dauka aiki, karon farko tun bayan da ya shirya wani dan gajeren yaki kan jami’an tsaron Rasha.
- Ta kashe dan kishiyarta kwana 4 da haihuwarsa a Bauchi
- Kungiyar Tarayyar Afirka ta dakatar da Nijar daga cikinta
A cikin bidiyon, Shugaban kamfanin na Wagner mai shekaru 62, ya ce suna gudanar da bincike don ganin cewa Rasha ta kasance a kan gaba a dukkan nahiyoyi.
Sai dai kamfanin dillancin Labarai na AP ya ce bai iya tabbatar da sahihancin bidiyon da kansa ba, wanda ya nuna Prigozhin yana tsaye a wani wuri tare da manyan motocin daukar kaya tare da wasu mutane sanye da kakin soji a bayansa.
Amma kafafen sada zumunta a Rasha da ke da alaka da shugaban kamfanin sun ce kamfanin na daukar ma’aikatan haya a Afirka tare da gayyatar mutane daga Rasha don zuba hannun jari a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Kamfanin na Wagner tun daga shekarar 2014, ya fara wanzuwa a fadin Afirka, kuma ana ganin gwamnatin Rasha na amfani da shi a matsayin wani makami na fadada karfin fada-a-jin da take da shi a Gabas ta Tsakiya da kuma nahiyar Afirka.