Rasha ta fara janyewa daga iyakarta da Ukraine
Ministan Tsaron kasar Ukraine ya ce dakarun kasar Rasha sun fara janye wa daga kan iyakokin kasar Ukraine, inda ya danganta janyewar da daukar matakan diflomasiyar da kasar Amurka ta yi kan rikicin.Ya yi wannan bayanin ne ranar Litinin da ta gabata. Sai dai kuma bai fadi yawan dakarun Rashan da suka janye daga kan […]
Ministan Tsaron kasar Ukraine ya ce dakarun kasar Rasha sun fara janye wa daga kan iyakokin kasar Ukraine, inda ya danganta janyewar da daukar matakan diflomasiyar da kasar Amurka ta yi kan rikicin.
Ya yi wannan bayanin ne ranar Litinin da ta gabata. Sai dai kuma bai fadi yawan dakarun Rashan da suka janye daga kan iyakokin ba, amma kasar Amurka da Tarayyar Turaisun ce yawan su ya kama daga dubu 30 zuwa dubu 40.
A ranar Litinin da ta gabata ne, wata Cibiyar Tsaron kasar da ke birnin Kieb ta ce dakarun Rasha dubu 10 ne kawai suka rage ba a janye ba a iyakoyin ta da Ukraine.