Rasha ta harba makamai masu linzami fiye da 40 kan Kyiv — Zelensky

MDD ta ce watan Yunin bana shi ne mafi muni ga fararen hula a Ukraine tun bayan watan Afrilun 2022, inda aƙalla mutum 293 suka rasa rayukansu.

Rasha ta harba makamai masu linzami fiye da 40 kan Kyiv — Zelensky

Mutum ɗaya ya rasa ransa, yayin da wasu 16 suka jikkata sakamakon ruwan makamai masu linzami da Rasha ta yi wa babban birnin Ukraine, Kyiv, cikin daren Lahadi, a wani hari da hukumomin Ukraine suka bayyana a matsayin ɗaya daga cikin mafi muni tun bayan fara yaƙin.

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce Rasha ta harba makamai sama da 40, ciki har da makamai masu linzami na ballistic guda 25, waɗanda galibinsu suka nufi Kyiv.

Ya ce hare-haren sun afku a unguwanni shida na birnin, inda suka lalata gine-gine ciki har da gidaje, manyan shaguna da cibiyar nishaɗi.

Wata mazauniyar Kyiv mai suna Ganna Zagorodnia ta ce ƙarar fashewar makaman ba ta katse ba tsawon dare.

Ta ce, “Makaman suna ta zuwa ɗaya bayan ɗaya, fashewar ta kasance mai ƙarfi matuƙa. Na yi zaton rayuwata ta zo ƙarshe.”

Da safiyar Lahadi, wakilan Kamfanin Dillancin Labarai na AFP sun ga gidajen da gobara ta cinye, tagogi da suka farfashe da kuma motoci da hare-haren suka kifar.

Sai dai Rasha ta ce hare-haren nata sun nufi sansanonin soji, cibiyoyin adana kayan yaƙi da kuma wasu muhimman wuraren sojin Ukraine a Kyiv da tashar jiragen ruwa ta Odesa, tana mai musanta zargin kai hare-hare kan fararen hula.

Zelensky ya sake yin kira ga ƙawayen ƙasarsa da su ƙara samar wa Ukraine makaman kariya daga hare-haren sama, musamman makaman da ake amfani da su wajen kakkaɓo makamai masu linzami na ballistic.

Ya ce ƙarancin makaman kariya na tsarin Patriot ya ba Rasha damar ƙara yawan hare-haren makamai masu linzami kan Kyiv a makonnin baya-bayan nan.

A gefe guda kuma, hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da dubban ’yan Ukraine ke ci gaba da gudanar da zanga-zanga a manyan biranen ƙasar, domin nuna adawa da matakin Shugaba Zelensky na sauke Ministan Tsaro, Mykhailo Fedorov, daga muƙaminsa.

A ɓangaren Rasha kuwa, hukumomi sun ce wani hari da Ukraine ta kai a yankin Kursk ya kashe mutum ɗaya.

Haka kuma, wani harin jirage marasa matuƙa da Ukraine ta kai ya lalata wasu tankokin dakon ɗanyen mai guda biyu a tashar Caspian Pipeline Consortium da ke kusa da tashar jiragen ruwa ta Novorossiysk a Tekun Black Sea, lamarin da ya tilasta dakatar da ayyukan jigilar mai.

A ranar Asabar ma, Ukraine ta ce ta kai hare-hare kan wasu manyan rumbunan adana kaya guda biyu a yankunan Moscow da Tambov, inda aka ruwaito mutuwar ma’aikata takwas da tashin gobara mai ƙarfi.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce watan Yunin bana shi ne mafi muni ga fararen hula a Ukraine tun bayan watan Afrilun 2022, inda aƙalla mutum 293 suka rasa rayukansu.

Yayin da ɓangarorin biyu ke ci gaba da musayar hare-hare, tattaunawar samar da zaman lafiya da ke gudana tana ci gaba da tangal-tangal.