Rasha ta kai hare-haren makamai masu linzami a Ukraine
Rabon da Rasha ta kaddamar da hari a Ukraine tun ranar 26 ga watan Yuni.
Wasu manyan biranen Ukraine sun wayi gari da hare-haren makamai masu linzami ciki da Kiev, Fadar Gwamnatin kasar.
Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan Rasha ta zargi kasar da kitsa fashewar da ta karya babbar gadar Kerchi ta yankin Crimea.
- An soma bincike kan mutuwar mutum 5 ’yan gida daya a Enugu
- Gwamnati za ta rage kashi 30 na cunkuso a gidajen gyaran hali
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ukraine, Kyrylo Tymoshenko ya ce baya ga Kiev, birane da dama sun wayi gari da hare-haren wanda zuwa yanzu ba a kai ga tantance adadin mutanen da suka mutu ba.
Tuni dai mahukuntan Ukraine suka umarci jama’a da su ci gaba da zama a gidajensu don kaucewa harin na Rasha.
Wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Faransa, ya bayyana cewa da misalin karfe 8:15 na safiyar yau Litinin ne aka rika jiyo karar fashewa kafin daga bisani a tabbatar da harin a birane da dama.
Rabon da Rasha ta kaddamar da hari a Ukraine tun ranar 26 ga watan Yuni.
AFP ya ruwaito cewa, guda cikin makaman roka da Rasha ta harbo ya sauka a gab da wata makarantar kananan yara.
Sai dai babu tabbacin ko ya kashe wasu daga ciki, sai dai bayanai sun ce an gano hayaki yana tashi a gab da makarantar.