Rasha ta kori jami’an diflomasiyyar Jamus sama da 20

Lamarin ya shafi huldarsu ta fuskar kasuwanci musanman kan batun makamashin gas.

Rasha ta kori jami’an diflomasiyyar Jamus sama da 20

Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin

A wani mataki na ramuwar gayya, Rasha ta kori jami’an diflomasiyyar Jamus sama da 20 a cewar mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha.

“Fiye da jami’an diflomasiyyar Jamus 20” aka kora daga Rasha, kamar yadda mai magana da yawun diflomasiyyar Rasha Maria Zakharova ta shaida wa gidan talabijin na Zvezda.

Ana kyautata zaton hukumomin Jamus za su shiga tataunawa da Rasha ganin cewa jami’an Rasha na ci gaba da aiki a Jamus.

Wannan matakin na zuwa ne bayan da Rasha ta sha alwashin mayar wa Berlin da martani mai zafi a game da matakin da ta dauka na korar wasu jami’an diflomasiyyarta.

Fadar Kremlin ta ce korar jami’anta ba zai taba yin wani tasiri ba illa ya kara dagula lamura a dangantakarsu.

Kyakkyawar dangantakar da ke a tsakanin kasashen biyu ta soma tsami, tun bayan da Rashan ta soma mamayar Ukraine a bara.

Haka kuma, kasancewar Jamus a sahun gaban kasashen Yamma da ke goyon bayan Ukraine, lamarin ya shafi huldarsu ta fuskar kasuwanci musanman kan batun makamashin gas.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50