Rasha ta nesanta kanta da zanga-zangar Najeriya

Ƙasar ta ce ba ta hannu a zanga-zangar da ake yi a Najeriya.

Rasha ta nesanta kanta da zanga-zangar Najeriya

Ofishin Jakadancin Rasha a Najeriya, ya bayyana cewa ba shi da wata alaƙa da masu zanga-zangar da ke ɗaga tutocinta a wasu sassan Najeriya.

Ofishin ya bayyana cewa ayyukan masu zanga-zangar ba sa wakiltar wata hukuma daga gwamnatin Rasha.

Yayin zanga-zangar da ake yi a ƙasar, wasu matasa a Arewacin Najeriya, sun dinga ɗaga tutar Rasha suna rera waƙoƙi tare da neman ɗauki.

Wannan ya haifar da damuwa dangane da zargin hannun Rasha a rikicin siyasa a wasu ƙasashen Yammacin Afirka kamar Mali, Burkina Faso da kuma Nijar.

Ofishin Jakadancin Rasha ya jaddada cewa Rasha tana mutunta tsarin kowace ƙasa kuma ba ta tsoma baki a harkokinsu na cikin gida.

Ofishin ya jadadda cewar amfani da tutar Rasha da masu zanga-zangar suka yi, ba komai ba ne face son rai kuma hakan ba shi da alaƙa da gwamnatin Rasha.

Duk da cewa ofishin yana goyon bayan zanga-zangar lumana, amma ya yi Allah-wadai da duk wani tashin hankali ko rikici.

Ofishin ya kuma tabbatar da girmama dimokuraɗiyyar Najeriya da kuma haƙƙin gudanar da zanga-zanga bisa doka da oda.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS