Rasha ta sace Daraktan Masana’antar nukiliyar Ukraine

Sojojin Rasha sun yi gakuwa da Mataimakin Darakta-Janar na Sashen Kula da Ma’aikta a Masana’antar Nukiliya ta Zaporizhzhia, Valeriy Martyniuk

Rasha ta sace Daraktan Masana’antar nukiliyar Ukraine

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zolenskyy

Sojojin Rasha da sun yi awon gaba da wani Dakarta-Janar da ke aiki a masana’antar nukiliyarta ta Zaporizhzhia.

Gwamnatin Ukraine na zargin dakarun Rasha da azabtarwa da kuma wulakanta babban jam’in a masana’natar nukiliyar da ke yakin Kudancin Ukraine da ke karkashin ikon sojojin Rasha.

“Sojojin Rasha sun yi gakuwa da Mataimakin Darakta-Janar na Sashen Kula da Ma’aikta a Masana’antar Nukiliya ta Zaporizhzhia, Valeriy Martyniuk,” in ji sanarwar da gwamnatin Ukraine ta fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta yi kira ga Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) Rafael Grossi da zai kai ziyara Rasha da ya sa baki Rasha ta sako jami’in.

An yi garkuwa da mutum 43 da kashe yaro a Sakkwato

Klopp zai maye gurbin Nagelsmann a matsayin kocin Jamus

Sojoji sun kama masu ƙera makamai a Kebbi

Bam ya kashe aƙalla mutum shidda a Siriya