Rasha ta yi ruwan bama-bamai a babban birnin Ukraine

Rasha ta yi ruwan makamai masu linzami a kan Kyiv, babban birnin makwabciyarta, Ukraine.

Rasha ta yi ruwan bama-bamai a babban birnin Ukraine

Luguden wutar da sojojin Rasha ke yi a Ukraine

Rasha ta yi ruwan makamai masu linzami a kan Kyiv, babban birnin makwabciyarta, Ukraine.

A ranar Alhamis ne dakarun Rasha suka yi wa birnin Kyiv luguden wuta, a karon farko cikin makonni.

Rahotanni sun ce hare-haren sun yi barna kuma Hukumar tara bayanan sirri ta sojojin Birtaniya an zargin rundunar Wagner group ya kai sabon harin.

Hare-haren, an kai su ne a kan cibiyoyin aikin soji a yankin Vyshhorod inda aka jikkata mutum 15, kamar yadda gwamnan Kyiv, Oleksiy Kuleba, ya sanar.

Harkokin sun fara komawa yadda aka saba a Kyiv, bayan gazawar sojojin Rasha su kwace birnin a farkon lokacin da suka kaddamar da mamayar Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu.

An kai sabon harin ne washegarin bikin zagayowar ranar samun ’yacin Ukraine, a daidai kuma lokacin da Shugaban Kasar Lithuanian, Gitanas Nauseda, yake ziyarar aiki a birnin Kyiv.

Rokokin Rasha guda 10 sun yi barna a yankin Chernihiv da ke Arewa maso Yammacin Kyiv a ranar Alhamis, kamar yadda gwamnan, Vyacheslav Chausov ya bayyana.

Rundunar sojin kasa da ke Arewacin Ukraine ta ce makamai masu linzami kusan 20 ne aka harbo daga yankin kasar Belarus zuwa Lardin Chernihiv, mai iyaka da kasar Rasha.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos