Rasha za ta taimaka wa kasashen Sahel
Rasha za ta taimaki kasashen yankin Sahel masu fama da kungiyoyin jihadi.
Rasha tana ci gaba da karfafa ikonta a kasashen Afirka inda ta yi alkawarin taimakon kasashen yankin Sahel na Afirka da ke fama da matsalolin tsaro.
A ranar Talata ce Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei Lavrov ya bayyana cewa kasarsa za ta taimaki kasashen yankin Sahel na Afirka da suke fama da matsalolin tsaro na kungiyoyin jihadi.
DAGA LARABA: Dalilin tallata kanmu a ‘Soshiyal Midiya’ don neman miji —’Yan Mata
Lavrov ya fadi haka yayin ziyarar da ya kai birnin Bamako na kasar Mali da ke yankin Yammacin Afirka.
Ministan ya ce Rasha za ta taimakin kasashen domin shawo kan matsalolin da suke ciki.
A shekara ta 2020 sojoji suka kwace madafun ikon Mali inda suka karkata hulda daga Faransa wadda ta yi wa kasar mulkin mallaka zuwa kasar Rasha.
Tun shekara ta 2012 kasar ta Mali ke fama da matsalolin tsaro daga kungiyoyi tsageru masu dauke da makamai da masu ikirarin jihadi.