Rashawa na ruguza kasa
Ana cin hanci da rashawa a ko’ina a duniya, amma ba kamar yadda ma’aikatun gwamnati suka mayar da cin hanci da rashawa wata dabi’a ba a Najeriya, abin kan bada tsoro. Kusan idan kana son biyan bukata ya zama wajibi ka biya ko ka kwan ciki! Wannan halaiya tasa akan gaza kididdige nawa aka kashe […]
Ana cin hanci da rashawa a ko’ina a duniya, amma ba kamar yadda ma’aikatun gwamnati suka mayar da cin hanci da rashawa wata dabi’a ba a Najeriya, abin kan bada tsoro. Kusan idan kana son biyan bukata ya zama wajibi ka biya ko ka kwan ciki!
Wannan halaiya tasa akan gaza kididdige nawa aka kashe ko aka aiwatar a kasafin ma’aikatu, ko nawa ake samu. Kuma ta kan haifar da ha’inci wanda kan rage nagartar kowane aikin da za a yi, a yi kwange ko a kimshe kaya su kasa yin karko.
Ba wani abu yake jawo cin hanci da rashawa ba illa kwadayi watau zari, neman dukiya fiye da dan uwanka, wanda hakan kan zama cuta, barna, sata, yaudara da zalunci. Cin hanci da rashawa, ba wata cuta ce da ake kamawa idan an sha kwaya ko wani magani, dabi’a ce, wadda ta zama jiki a jinin dan Najeriya.
Tabbas abin kunya ne, a ce cin hanci da rashawa sun zama tsarin tafiyarwa a Najeriya, haka na nuna cewa sai an yi gagarumin yaki a kawo karshen wannan fitinar, wadanda basu fada cikin wannan hadarin ba, na jin kanshin rashawa da hancinsu, suna kallon ta tana burge su, watau yara da mata, su dai iyayensu ko mazaje su samo kudi a ji dadi! Ba ruwan matarka da ‘ya’yanka ko sata ka yi kai dai ka kawo kudi a ji dadi, su dai daura gwal, a sauya kayan daki, a gasa kaji, a ci nama, a sa su a makaranta mai tsada, a kai su a latsetsiyar mota, shikenan. A nan ba a maganar talakawa, masu nema ido rufe! Watau wani abin mamaki ma shi ne wai ta yaya iyayenmu da kakani suka rayu ba tare da tara abin duniya ba?
Babu bambanci tsakanin karamin barawo da barawon biro ko barayin gwamnati, duk darayi ne, da wanda ya sha giya ta Naira daya da wanda ya sha ta dubu, duk mashaya ne! Mu fahimci idan ka ba ma’aikacin Nepa kudi don kar a tsinka ma waya, ai baka biya bil ba, dukkanku sun fada cikin cin hanci da rashawa, da kai da ka bada da shi da ya karba. Ladan ya ci kudin masallaci, ko mace ta kara ko rage wani abu a kudin cefane, cin hanci da rashawa ne.
Hakan ke sa mutane kadan ke kai kukansu kotu ko chaji ofis, don gudun fadawa cikin wani cinikin! Domin alkalai da ‘yan sanda ne neman hancin wasu ma fuskar za su cinye! Jira ake ruwa a jallo!
Maganar ita ce nawa zaka biya, domin kudi ke magana, wasu kan yi toshiya da kayan abinci ko abubuwan sha ko wasu alfarmomi don tabbatar da an samu ‘yanci ko an yi danniya, yayin da wani lokacin akan yi cuda-ni-in-cude ka, kamar tsakanin malaman jami’a da dalibai da dai sauransu. Abin ya kai har malaman addini ake biya wa Hajji ko Umra don su yabi wani kasurgumin barawo, ko ku ga an gina masallaci ko islamiyya duk da kudin sata don a wanke mutum a idon mutane! Koda sadaka ce, musamman ga wanda yake kyamar mutane.
Wani lokacin irin wannan musaya ko cudanya kan shafi mutuntakar ‘ya mace ko ta sa mutum ya yi kawalci don ya biyawa ubangidansa bukata shi ma ya sami bukatarsa! A koina ka tsinci kanka a makaranta, asibiti, kasuwa, kai har a makabarta ana rashawa!
Bincike ya tabbatar da cewa babu abin da ya fi zama barazana gatarayyar Najeriya kamar cin hanci da rashawa, wadda ke neman cinye kasar baki daya, kuma idan gwamnati da ‘yan kasa ba su yi nasara ba kan wannan fitinar to Najeriya ta hau hanyar hallaka.
Wani abin dubawa shi ne hatta malamai kan nunawa dalibai cewa da karatu ake samun kudi ko neman duniya, maimakon ilimi a matsayin hanyar wayewar kai da warware matsaloli, domin daga al’umma. Wannan karkataciyyar basirar tasa kudin sun shiga gaban iyaye ta yadda ko a ‘ya’yansu sai su rika bautawa attajiri. Bayan a zahiri ‘yan kasuwa aka sani da juya kudi, su ya kamata gwamnati ta rika karfafawa da jari fiye da nuna ana sakawa matasa da sadaka a sunan sukolashif!
Babban abin takaici game da kasar shi ne alkalai a ma’aikatun shari’a wadda nan ne inda za ka kai kukan karshe, ga ‘yan sanda wadanda idan aka fi karfin ka za su kare ka, amma sun fi kowa fadawa cikin cinikin! Kar ku manta akwai ‘yan kwangila masu aringizo, kuma wani lokaci ka ga suna taimakon talakawa da kudin da suka handame!
Aiki ’yan sanda ne su kama duk wanda ya karya doka ko oda, a gafatar a wajen lauya ko joji wadanda sune jagororin shari’ar amma alkalan sun nuna rauni wajen ba su iya hakuri su ba mai gaskiya gaskiyarsa! To inda za ka je, kuma mene ne makomar kasar?
Maimakon kafa wasu sababbin kwamitoci don sa’ido, ita kanta hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) da banagren ‘yan sanda da mujiramai ICPC sun isa, idan aka dauke siyasa daga aikin, kuma aka fadada yadda za a tunkare wannan bala’in.
Tabbas akwai hanyoyin da za mu iya yakar cin hanci da rashawa, mu yi nasara, kuma wannan rana na kusa. An samu ci gaba a yaki da cin hanci da rashawa, a yau kowa ya tabbatar da cewa shugaban kasa ba barawo ba ne, gwamnoni sun rage gadara, “caimomi babu camama,” sannan babu kansiloli balle su sace dukiyoyinmu. Sabanin da wanda shugaban kasa barawo, gwamnoni barayi, kai karamin ma’aikaci jira yake ya samu dama, kuma a dinga bin barayin da ranka ya dade. Duk da haka akwai aiki a gaba, gagarumin aiki wajen dakile wannan fitinar, domin ana yaki, shi ma cin hancin da rashawar na yaki da mutanen, ta yadda ko jami’an yaki da cin hanci da rashawan abin zargi ne!
Cin hanci da rashwa sun haifar da zargi, kowa na zaton dan uwansa da wani laifi, musamman idan attajiri ne, ko don abin da ya mallaka ya fi karfin albashinsa, daga cin zabe! Ko wa ya ba shi jari? A cikin zukatanmu, ba mu yarda da juna ba, wani abin takaici ma shi ne, mu kan daukaka mabarnata, domin su ne mawadata a al’umma, muna zama tare cikin yunwa da talauci. Hadarin shi ne kowa na son zama kamar wadannan mutanen!
Ya kamata hukumomin yaki da cin hanci da rashawa su hada kai su yaki wannan fitinar, a kawo gyara, a hukunta mabarnata, a tsaurara dokoki, kuma a aiwatar ta yadda za a fita daga zargin, ana yakin son rai ko a kafofin yada labarai ake yaki da cin hanci da rashawar, domin idan ba a fito aka yaki wannan barazanar ba gaba da gaba ba, za a ci gaba da zargi!
Ina fata zamu wayi gari beli ya zama kyauta a zahiri ba a rubuce ba! Ranar da ma’aikatan Nepa ba zasu rika karbar kudi ba a sunan na wuta fiye da abin da aka yi amfani da ita a bil. Ranar da malami zai rubuta jarrabawa ya bar dalibai, ba tare da wani ya halin beraye ba.
A karshe ina ganin idan da iyaye da maluma za su fifita neman ilimi a bisa neman kudi da mulki, domin da ilimi ne zukata suke samun natsuwa, da an haifi al’umma mai tarbiyya da nagarta. Amma neman duniya, son girma a ce kai ne, ka tara kudi, mukamai ko mulki na jawo kowace irin fitina wadda ta hada da gaba da gasa masu tabbatar da cin hanci da rashawa. Amma ranar da muka bi hanyar ilimi mai amfani da mu’amala mai kyau, mun yi galaba kan rashawa.
Buhari Daure [email protected]