Rashawa ta jefa jama’a cikin kunci da fatara – Gwamnan Neja
Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya ce cin hanci da rashawa da aka dade ana ado da su a tsakanin ’yan siyasa da ma’aikatan gwamnati ne suka jefa akasarin jama’ar kasar nan cikin fatara da kuncin rayuwa.Gwamna Abubakar Sani Bello ya ce al’amarin yana da ban takaici ganin yadda mutane kalilan suka yi […]
Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya ce cin hanci da rashawa da aka dade ana ado da su a tsakanin ’yan siyasa da ma’aikatan gwamnati ne suka jefa akasarin jama’ar kasar nan cikin fatara da kuncin rayuwa.
Gwamna Abubakar Sani Bello ya ce al’amarin yana da ban takaici ganin yadda mutane kalilan suka yi ta watanda da dukiyar da ta wajaba a samar wa jama’a muhimman abubuwan inganta rayuwa da suka hada da hanyoyi da asibitoci da makarantu da takin zamani da kayan aikin gona da sauransu.
Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da yake rantsar da shugabannin kananan hukumomin jihar 24, inda ya tunatar da su cewa yanzu lokacin siyasa ya wuce, abin da za su sa a gaba shi ne yadda za su inganta rayuwar mutanensu, kamar yadda manufofin Jam’iyyar APC suka tanada.
Gwamnan ya bukaci shugabannin su yi aiki kafada-da kafada da shugabannin jam’iyyar da shugabannin rikon kwarya da za su mika musu mulki don cimma nasara. Kuma ya shawarce su su rika zama a cikin jama’arsu domin sauraren koke-kokensu tare da shawo kan matsalolin da suke ci musu tuwo a kwarya.
Gwamna Abubakar ya nemi al’ummar jihar su rika tambaya kan yadda ya sarrafa kudin da jihar ke samu daga kason tarayya, inda ya ce ya adana bayanan yadda ya sarrafa kowane kwabo da sisin jihar tun daga hawansa mulkin jihar.