Rashawa ta yi katutu zamanin Buhari – Bishop Kukah

Bishop na ɗariƙar Katolika a yankin Sokoto, Mathew Hassan Kukah ya ce ba a taɓa cin rashawa a Najeriya kamar zamanin mulkin shugaba Muhammadu Buhari ba. Bishop Kukah ya bayyana haka ne ranar Litinin a jawabin da ya gabatar wurin bikin cikar Aare Afe Babalola SAN shekaru 60 da zama lauya. Limamin cocin ya ce […]

Rashawa ta yi katutu zamanin Buhari – Bishop Kukah

Bishop na ɗariƙar Katolika a yankin Sokoto, Mathew Hassan Kukah ya ce ba a taɓa cin rashawa a Najeriya kamar zamanin mulkin shugaba Muhammadu Buhari ba.

Bishop Kukah ya bayyana haka ne ranar Litinin a jawabin da ya gabatar wurin bikin cikar Aare Afe Babalola SAN shekaru 60 da zama lauya.

Limamin cocin ya ce duk da dai ba a mulkin Buhari aka  fara cin rashawa a Najeriya ba, amma lamarin yafi muni a zamaninsa.

Buhari ya gama lalata rayuwar ’yan Najeriya —Bishop Kukah

Matthew Kukah ya sake caccakar gwamnatin Buhari

Ya ce ‘A waccan gwamanatin mun ga mafi nunin cin rashawa ta fannin tarbiyya, hada-hadar kuɗi, da ma fannoni da dama.’

Bishop Kukah ya kuma koka da yadda shugabannin suke tattare ayyukan ci gaban al’umma zuwa yankunan da suka fito.

Ya ce hakan ba zai taimaka wurin bunƙasa dimokraɗiyya a Najeriya ba.