Rashidi Yekini ya cika shekara uku da rasuwa

Tsohon dan kwallon gaba a kungiyar kwallon kafa ta kasa Rashidi Yekini ya cika shekara uku da rasuwa. An yi addu’ar cikarsa shekara 3 da rasuwa ne a ranar Litinin da ta gabata a Legas. Yekini ya rasu ne a ranar 4 ga watan Mayun shekarar 2012. A tattaunawa da wakilin Aminiya ta waya, daya […]

Rashidi Yekini ya cika shekara uku da rasuwa
Rashidi Yekini ya cika shekara uku da rasuwa

Tsohon dan kwallon gaba a kungiyar kwallon kafa ta kasa Rashidi Yekini ya cika shekara uku da rasuwa. An yi addu’ar cikarsa shekara 3 da rasuwa ne a ranar Litinin da ta gabata a Legas. Yekini ya rasu ne a ranar 4 ga watan Mayun shekarar 2012.

A tattaunawa da wakilin Aminiya ta waya, daya daga cikin ’yan kwallon Super Eagles a da, Garba Lawal ya bayyana Rashidi Yekini a matsayin da dan kwallon da ba a taba yin irinsa a kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles ba.
“Tun a shekarar 1998, watau kimanin shekaru 17 da suka gabata kawo yanzu, ba a samu dan kwallon gaba da ya kama kafarsa balle a ce ya wuce shi a kungiyar Super Eagles ba, inji Garba Lawal.
Yadda marigayin ya buga kwallo a lokacin da yake raye, a gaskiya ba na jin za a sake samun kamarsa a nan kusa, sai dai ban san nan gaba ba ko za a iya samu.
Rashidi Yekini yakan zura kwallaye a raga ne a wani yanayin na musamman da ba kowane dan kwallo ne zai iya yin haka ba. Ya fara haskakawa ne tun yana kulob din masakar UNTL da ke Kaduna kafin ya samu daukaka zuwa kulob da dama a ciki da wajen Najeriya”, inji shi.
Rashidi ya yi wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles wasa har sau 58 inda ya samu nasarar zura mata kwallaye a raga har sau 37 a tsakanin shekarun 1984 zuwa 1998. Shi ya fara zura wa Najeriya kwallon farko a ragar Bulgariya a gasar cin kofin duniya a shekarar 1994 a Amurka, bayan Najeriya ta lallasa Bulgariya da ci 3-0.
Haka kuma marigayin ne ya zama dan kwallon da ya fi zura kwallaye a raga a gasar cin kofin Afirka da aka yi a Tunisiya a shekarar 1994, kuma a shekarar ce Najeriya ta samu nasarar lashe kofin.
Idan za a tuna marigayin ya mutu ne a Ibadan a wani mummunan yanayi saboda rashin kudi da kuma kulawa daga Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) duk da irin daukaka suna da martabar Najeriya da ya yi a idon duniya.