Rashin ababen hawa: An yi bikin sallah cikin kunci a Borno da Yobe

Takaita zirga-zirgar ababen hawa ya rage wa bukukuwan babbar Sallah armashi a  jihohin Borno da Yobe saboda matsalar tsaro . A Maiduguri tun da safiyar ranar sallar, wato ranar Asabar, mutane da dama suka yi  ta taka sayyada  zuwa filayen  idin da ke Unguwanni daban-daban, irin su filin sukuwa da harabar  filin ‘yan sanda da filin […]

Rashin ababen hawa: An yi bikin sallah cikin kunci a Borno da Yobe

Takaita zirga-zirgar ababen hawa ya rage wa bukukuwan babbar Sallah armashi a  jihohin Borno da Yobe saboda matsalar tsaro .
 A Maiduguri tun da safiyar ranar sallar, wato ranar Asabar, mutane da dama suka yi  ta taka sayyada  zuwa filayen  idin da ke Unguwanni daban-daban, irin su filin sukuwa da harabar  filin ‘yan sanda da filin Polo, da na Jami’ar Maiduguri, da dai sauransu, inda aka gudanar da sallolin cikin kwanciyar hankali duk da tsauraran matakan tsaron da jami’an tsaro suka dauka na gudanar da binciken kwakwaf ga kowane mutumin da zai shiga wadannan filayen Idin.
Armashin  Sallar  a garin Maiduguri ya ragu kwarai saboda  takaita zirga-zirgar ababen hawa a unguwanni da manyan tituna, wanda ya sanya babu zuwa sallar idi a ababen hawa, babu ziyace-ziyarcen ‘yan uwa da abokan arziki kamar yadda aka saba kuma ake yi a kowace shekara, haka aka zauna a cikin wannan halin har na tsawon kwanaki 3.
Bugu da kari kuma Mai martaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Umar Garbai Al -Amin El-kanemi, shi ma ya soke gudanar da hawan sallar da aka saba yi a fadarsa duk shekara, kodayake  a lokcin karamar  sallar da ta wuce ma ba a yi irin wannan hawan ba, wanda hakana ba ya rasa nasaba da dalilan rashin tsaro,  domin tun a ranar jajibarin Sallah jami’an tsaro suka fitar da sanarwa da ke cewa za a takaita zirga-zirgar ababen hawa har na tsawon kwanaki 3, duk da cewar al’ummar garin Maidugurin sun bayar da cikakken hadin kai tare da amincewa da wannan dokar kamar yadda ya faru a karamar Sallar da ta wuce, amma a hakikanin gaskiya dokar ta takura wa  Jama’a da dama a birnin, kamar dai yadda wakilinmu ya ji daga wadansu mazauna garin na Maiduguri.
 Malam Babagana Bukar  cewa ya yi ; ‘’A gaskiya ba mu ji dadin takaita zirga-zirgar nan a wannan sallar ba, domin ya takaita mana sada zumunci, duk da cewar mun tsinci kanmu a cikin halin rashin tsaro, amma ya takaita mana gudanar da harkokin rayuwarmu na yau da kullum, musamman a irin wannan lokaci na farin ciki, domin ni ina dauka a yanzu za a iya cewa komai ya lafa a garin Maiduguri, Jami’an tsaro za su barmu mu gudanar da harkokin sallarmu kamar yadda muka saba,  amma a yanzu a gaskiya ina jin kamar ba sallah na yi ba, domin ba zai yiwu a ce sallah gaba daya, wadda daga shekara sai shekara ake gudanarwa, sannan kuma ka hana mutum zuwa sallar idi a  mota kuma ka hana sada zumunci,  a ce wai an yi sallah,  amma dai muna rokon Allah Ya kawo mana karshen wannan mummunan tashin hankalin da muke fama da shi.’’
 Hajya  Falmata kuwa cewa ta yi, ‘’ ziyarar ‘yan uwa da abokan arziki tana daya daga cikin murnar sallah, to yau an ce kar mu yi , ai mun zama kuramen karfi da yaji ke nan a gidajenmu, duk da cewa ba ma son tashin hankali irin na ‘yan ta’adda kuma ba ma goyon bayansu, amma muna goyon bayan matakan da jami’an tsaro ke dauka na tabbatar da zaman lafiya a wannan gari namu, amma a gaskiya an takaita mu, mun kuma zama kurame da sallah, muna kuma rokon Allah Ya kawo karshen wannan bala’in.’’
 Shi kuwa Malam Modu Kachallah cewa ya yi, ‘’baya ga hana mu sadar da zumunci lokacin sallah, an kuma hana ni neman abincina, domin kuwa na kan yi amfani da irin wannan lokacin in kasa kayan sana’ata a kasuwa da wuraren da na san jama’a ke taruwa a irin wannan lokaci na bikin sallah.  Saboda haka babu abin da zan ce sai dai addu’a, Allah Ya kawo karshen wannan masifar da ta addabe mu. Amma a gaskiya ban ji dadin yadda jami’an tsaro suka garkame mu a gida ba fita ba, domin abin hawa ne kafar mutane a wannan lokacin kuma da shi ne za mu je mu nemi abinci. Ko da ko mutum bai mallaki abin hawa ba, da na haya ya dogara, ai wani sai ya fita yake samu, ga shi akwai nisa daga wadansu unguwannin zuwa wadansu, misali mutum zai tashi ne daga Bulunkutu ko Gomari ya zo Post Ofis ko Monday Market a kafa ya nemi abinci? ai ka ga ba za ta yiwu ba, to saboda haka Allah Ya kabe mana fitina.’’
 Wani matashi mai suna Sani Aliyu, cewa ya yi, ‘mun saba zuwa wasannin sallah ni da abokaina har gidan Zoo, da gidajen shakatawan da aka killace saboda irin wannan rana, amma a wannan sallar da kuma karamar sallar da ta wuce ba mu je ba saboda babu zirga-zirgar motoci, kuma ba za mu iya tafiya a kasa ba saboda akwai nisa,  amma idan an dage dokar ko bayan sallah ne sai mun tafi wadannan wuraren, domin a yanzu ina jin kamar ba sallah aka yi ba, sai na tafi wadannan wuraren sannan na san na yi bikin sallah.’’
Daga Damaturu kuma wakilinmu ya ruwaito cewa, al’ummar jihar Yobe sun gudanar da bukuwan sallah babba cikin kuncin rayuwa saboda jami’an tsaro na hadin gwiwa (JTF) sun sa dokar  hana zirga-zirgar ababen hawa na kwanaki hudu a fadin jihar, inda dokar ta fara aiki  daga ranar jumu’a 3 ga watan Oktoba zuwa ranar litinin 6 ga wata, daga bisani aka kara kwana daya ya zama sai ranar talata 7 ga watan na Oktoba ne al’ummomin suka samu sakewa.
 Wannan dokar ta haifar wa da al’umma shiga halin kunci ga rayuwa, ba ga al’ummar jihar  da aka yi dokar domin sub a, har  wadanda ke amfani da hanyoyin  gwamnatin tarayya da suka ratsa jihar ta shafa, ta yadda ma u ababen hawa ala tilas suka dakatar da tafiya.
 Wani direban tirela mai suna Malam Umaru Bahadeje ya shaida wa Aminiya cewa, a gaskiya su kam ba a yi musu adalci ba, domin kuwa  a cewarsa, ya dauko kaya ne a motarsa da niyyar idan ya je ya sauke a Maiduguri zai gaggauta ya koma garinsu a jahar Jigawa don yin bikin sallah shi da iyalensa, amma hakarsa ba ta cim ma ruwa ba, ag a kuma iyalensa da ke gida ba su da abin yin sallar, tunda dukannin kayansu suna wurinsa. Don haka ya ce akwai bukatar nan gaba idan  za a sa irin wannan doka  a sanar da al’umma tun da wuri .
Shi kuwa Usman Mai kayan  yara da ke da zaune a Damaturu cewa ya yi,, wannan doka ta hana walwala da aka sa musu babu laifi, sai dai kuma ba a yi la’akari da wadansu abubuwa ba  kafin kafa dokar, domin kuwa shigar sauri aka yi musu, kasancewar ba su tanadi komai ba na hidimomin sallah, don mafi yawan jama’a ba su tanadi dabbobin da za su yanka ba a hannunsu sun bari sai a ranar jajibere ne za su saya, sai kuma aka kafa musu wannan dokar a ranar.
A ganinsa wannan irin shigar sauri da hukumomin tsaro suka musu ba su ji dadinsa ba, duk da cewa a tsarinsu daidai suka yi, amma ga talakawa ai an sa su cikin kunci ne, dama can suna cikin tsakar tsadar rayuwa sai kuma aka sanya su cikin wani kuncin. Don haka akwai bukatar nan gaba hukumar tsaro ta taimaka ta rika yin hannunka mai sanda kafin sanya irin wannan doka don kauce wa shiga irin halin da suka samu kansu a ciki.
 Malam  Hassan mai sayar da kayan gwari shaida wa Aminiya ya yi cewa, wannan dokar ta haifar musu da babbar asara, musamman ga su  masu sana’ar sayar da kayan gwari, domin kuwa sun tura a sayo musu irin kayayyakin da suke sayarwa amma motar da ke dauke da kayayyakin nasu an tsayar da ita, direban ya gaza shigowa cikin jihar,  ga shi kusan duk abubuwan da aka sayo musu, irin su tumatiri da taruhu da makamantansu, sun  lalace,  hatta kudin motar da suka yi alkawarin za su biya direban da ya dauko musu kayan ma sun gaza biya. Don haka ya roki hukumomin tsaro da su yi wa Allah nan gaba su rika sanar da jama’a yiwuwar sanya wannan doka a lokaci irin wannan don su san  yadda za su yi, duk da cewa sanya wannan doka ta yi daidai.
 Wani matashi da ya nemi a sakaye sunansa da ke yin kamasho a tashar motar Damaturu kokawa ya yi, inda ya bayyana cewa, sun sha matsananciyar wahala a lokutan da aka sanya wannan doka,  saboda a kullum ne suke fitowa su yi wa mota lodi domin  su samu abin kashewa, don haka sun fada cikin mawuyacin hali a kwanakin da aka yi ba tare da zirga-zirgar  motoci ba.
Duk da cewa takaita zirga-zirgar ta rage wa bikin sallar armashi, amma kuma masallatan idin da ke garin Damaturu sama da 7 sun yi cika makil da mutane saboda mutane da yawa ba su samu damar tafiya garuruwansu ba kamar yadda suka saba don yin bukuwan sallar.
Da Aminiya ke tuntubi kakakin rundunar tsaro na JTF  a jahar ta Yobe, Kaftin Eli Lazarus, a kan rashin sanar da jama’a kafin a kafa wannan dokar don su shirya, sai ya amsa da cewa, ai tsarinsu na tsaro ba haka ya ke ba, illa dai sun tabbata cewa dukan abin da suke yi suna yi ne don jama’a, kuma cikin yardar Allah  kwalliya na ci gaba da biyan kudin  sabulu. Sai dai suna rkkon jama’a da su ci gaba da ba su hadin kai.
 Shi ma mataimakin gwamnan jahar Injiniya Abubakar Ali a jawabinsa lokacin da sarakunan jahar  suka kai masa ziyarar gaisuwar sallah a madadin gwamnan jahar Alhaji Ibrahim Gaidam, ya nemi jama’a da  su ci gaba danuna  juriya dangane da wannan lamari, kuma ya hore su su zama masu bin doka da oda kamar yadda suke yi a kullum.
A sakonninsu na sallah ga al’ummaomin masarutunsu, masu martaba sarakunan Fika da Damaturu sun nemi jamaa da su zama masu son juna da ci gaba da bada gudummawa wajen  samar da zaman lafiya a jahar Yobe da ma kasa baki daya.
Da ya ke jawabi ga al’ummar masarautarsa jim kadan da kammala sallah a garin Potiskum, Mai martaba Sarkin Fika kuma shugaban Majlisar sarakunan jahar Yobe, Alhaji Abali Muhammad Ibn Muhmmad Idrisa ya nemi iyaye da su yi kokarin tura yaransu makarantu da zarar an bude saboda neman ilmi babban aiki ne ga kowa, musamman ma ga iyaye, ganin cewa su ne Allah (SWT) Ya dora wa  nauyin kiwon  ‘ya’yansu kuma  za a tambaye su yadda suka gudanar da kiwonsu idan alkiyama ta tsaya.
Shi ma a jawabinsa ga al’ummar masarautarsa, Mai martaba Sarkin Damaturu Alhaji Shehu Hashimi Ibn Al-Amin El-kanemi  ya hori al’umma ne da su ci gaba da addu’a domin al’amura su daidaita.  Ya kuma yi addu’ar Allah (SWT) Ya sa maniyyatan jahar su dawo gida cikin koshin lafiya.