Rashin abinci mai gina jiki ya hallaka yara 30 a Nasarawa
A kalla kananan yara 30 ne suka rasa rayukansu yayin da sama da 200 kuma suke jinya a asibitoci daban-daban da ke Jihar Nasarawa sakamakon rashin wadatattun abinci masu gina-jiki. Shugabar Cibiyar Kula da Lafiyar Kananan Yara ta Jihar Nasarawa, Hajiya Halima Yusuf ce ta sanar da haka a jawabinta a wajen wani taron yini biyu […]
A kalla kananan yara 30 ne suka rasa rayukansu yayin da sama da 200 kuma suke jinya a asibitoci daban-daban da ke Jihar Nasarawa sakamakon rashin wadatattun abinci masu gina-jiki.
Shugabar Cibiyar Kula da Lafiyar Kananan Yara ta Jihar Nasarawa, Hajiya Halima Yusuf ce ta sanar da haka a jawabinta a wajen wani taron yini biyu da cibiyar samar da abinci mai gina jiki ta gwamnatin jihar ta shirya da aka gudanar a Lafiya.
A cewar Hajiya Halima Yusuf yanzu an rarraba wadannan yara ne a cibiyoyin samar da magunguna na gwamnati guda 15 a jihar, sakamakon karuwar wannan rashin abinci mai gina jiki a cikin abinci da yaran ke ci da wasu cututtuka da suka haddabi yaran.
A kan haka ne ma a cewarta ya sa cibiyar ta yanke shawarar rika shiryawa da gudanar da tarurrukan wayar da kan al’ummar jihar baki daya, musamman mazauna yankunan karkara game da bukatar a rika bai wa kananan yara abinci mai gina jiki wadanda a cewarta suka hada da wake da nama da kifi da kwai da alale da madara da sauransu, don magance annobar da a yanzu ya zame ruwan dare a tsakanin kananan yara a jihar baki daya.
Daga nan sai ta bukaci cibiyar samar da abinci masu gina jiki na gwamnatin jihar ta rika tallafa wa kananan yara da ire-iren abincin a gidaje da makarantunsu don magance matsalar kasancewar yara su ne manyan gobe kuma bai dace ana rasa su ta irin wannan sakaci ba. A jawabinsa, Ko’odinetan Cibiyar Samar da Abinci Masu Gina Jiki na Gwamnatin Jihar, Abdul Osama ya bayyana muhimmancin da ke da akwai na ci gaba da wayar da kawunan al’umma baki daya dangane da bukatar su rika bai wa ’ya’yansu abinci masu gina jiki, inda ya ce a kan haka ne ma ya sa cibiyar ta sha alwashin ci gaba da gudanar da ire-iren wadannan tarurruka a kai-a kai.
Ya kara da cewa lokaci ya yi da ya kamata gwamnati a nata bangaren ta rika ware kasafin samar da abinci mai gina jiki ga kananan yara a jihar musamman daga kasafin kudinta na shekara-shekara don rigakafi ko magance matsalar a jihar. Daga nan sai ya yi alkawarin cewa zai isar da sako ga gwamnati don daukar matakan da suka dace a kan lamarin cikin gaggawa.
Taron ya samu halartar kwamitocin abinci masu gina jiki daban-daban da ke kananan hukumomin jihar 13 da ’yan jarida da ma’aikatan gwamnati da manoma da makiyaya da ma’aikatu masu zaman kansu da sauransu.