Rashin abinci ya tilasta daliban sakandare yin bara a Taraba
Rashin wadataccen abincin a makarantar sakandaren musanyar dalibai da ke Jalingo a Jihar Taraba ya tilasta wa daliban makarantan yin bara. daruruwan daliban wadanda suka fito daga jihohin Arewa 19 da ke karatu a makarantar sakandaren na bi gida-gida suna barar abinci. Binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa da yawa daga cikin daliban […]
Rashin wadataccen abincin a makarantar sakandaren musanyar dalibai da ke Jalingo a Jihar Taraba ya tilasta wa daliban makarantan yin bara. daruruwan daliban wadanda suka fito daga jihohin Arewa 19 da ke karatu a makarantar sakandaren na bi gida-gida suna barar abinci.
Binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa da yawa daga cikin daliban ba sa samun abinci sau biyu a rana, yayin da wasu daliban da ke aji daya zuwa biyu ke kwana ba su ci abinci ba, saboda a mafi yawan lokuta manyan dalibai na kwace musu dan abincin da suka samu.
Makarantar wadda ake kira Sakandaren Comprehensibe, an gina ta ne don ta dauki daliban da ake turo wa daga jihohi 19 na Arewa a karkashin wani shiri da jihohin suka bullo da shi don inganta zumunta a tsakanin dalibai ’yan asalin jihohin.
Binciken ya nuna cewa bayan rashin isasshen abinci akwai matsalar rashin ruwan sha da wurin kwana mai kyau, sannan makarantar ba ta da dakin magani, inda a wasu lokuta dalibai da kansu ke yin karo- karo don jinyar dan uwansu in ya kamu da rashin lafiya. Aminiya ta gano cewa daliban kan nemi taimakon kudi daga makwabtan makarantar don jinyan ’yan uwansu.
Wani abin tausayi shi ne yadda daliban da ke azumi ke fuskantar karancin abin bude baki da sahur, lamarin da kan tilasta su neman taimakon abin bude-baki a gidajen jama’a wasu kuma su tafi masallatai inda suke wasoso da almajirai.
A yanzu haka daliban da suka kammala karatu a makarantar sun kasa komawa jihohinsu saboda gwamnatin jihar ta gaza bayar da kudin motar da za a maida su.
Wasu daliban da wakilinmu ya zanta da su sun nuna takaici kan yadda ake wulakanta su a jihar ta duk da kasancewar ’ya’yan jihar da suke karatu a jihohinsu ana kura da su yadda ya kamata. Babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Mista Williams Lamu ya shaida wa wakilinmu cewa makarantar ta musaya ta Jalingo tana fuskantar rashin kudin gudanarwa daga gwamnati wanda ya sa ba a iya kula da daliban yadda ya kamata.
Ya ce an dauki tsawon lokaci ba a biya dan kwangilar da ke samar da abinci a makarantar ba saboda rashin kudi, kuma dan abin da ake ba daliban shugaban makarantar ne ke taimakawa. Mista Williams Lamu ya nuna takaicin kan yadda daliban makarantar ba sa samun isasshen abinci da sauran ababen jin dadi, ya ce suna da labarin irin halin da daliban ke ciki wanda ya sa ma’aikatar ta rubuta takardar neman kudi ga gwamnati don magance matsalar amma har yanzu ba a bayar da kudin ba.
Babban Sakataren ya ce rashin kudi ne ya hana a mayar da daliban da suka kammala karatunsu a makarantar zuwa jihohinsu kamar yadda sauran jihohi suka dawo musu da dalibansu.
“Yaran nan sun zu ofishina sun nemi a taimaka a koma da su jihohinsu, amma hakuri kawai na ba su domin ba mu da kudi,” inji Mista Lamu.