Rashin adalci da gudanar da mulki ke kawo kisan gilla a Najeriya – Sule Lamido
Dan takarar Shugaban kasar Najeriya daga jam’iyyar PDP, tsohon Gwamnan Jigawa Alhaji Sule Lamido ya bayyana abubuwan da suke haddasa kisan gillar da ake yi a matsayin rashin adalcin gwamnati ne wajen gudanar da mulki. Lamido, ya bayyana hakan ne a wani taron shugabannin kudancin da yankin tsakiyar Najeriya da aka jiya litinin a Abuja […]

Dan takarar Shugaban kasar Najeriya daga jam’iyyar PDP, tsohon Gwamnan Jigawa Alhaji Sule Lamido ya bayyana abubuwan da suke haddasa kisan gillar da ake yi a matsayin rashin adalcin gwamnati ne wajen gudanar da mulki.
Lamido, ya bayyana hakan ne a wani taron shugabannin kudancin da yankin tsakiyar Najeriya da aka jiya litinin a Abuja ya bayyana wa manema labarai bayan ganawar da suka yi cewa, jam’iyya mai mulki ta APC ta gaza kawo karshen kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.
Tsohon Gwamnan ya ce, tsarin mulkin kasar Najeriya na ci gaba da wargaje wa sakamakon rashin adalcin da ake yi na gudanar da mulkin kasar.
Lamido ya kara da cewa, duk wadannan garkuwan da ake yi da kisan gilla a jihohin Taraba da Adamawa da Zamfara da Sokoto da sauran shiyyoyin Najeriya rashin adalci ne. Bai kamata ace hakan na faruwa ba a tsarin dokar kasa, don haka ba bu wani adalci da shugabanni ke yi wa ‘yan kasar.