Rashin adalci ne a dora wa gwamnatin Buhari laifin matsanacin halin da ake ciki – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce rashin adalci ne a dora laifin matsanancin halin da ake ciki a kasar nan a kan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ’yan […]

Rashin adalci ne a dora wa gwamnatin Buhari laifin matsanacin halin da ake ciki – Sheikh Jingir
Rashin adalci ne a dora wa gwamnatin Buhari laifin matsanacin halin da ake ciki – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce rashin adalci ne a dora laifin matsanancin halin da ake ciki a kasar nan a kan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a garin Jos, inda ya ce kowa ya sani a gwamnatin baya tsaro da  tattalin arziki duk sun rushe, amma a ki tuno wadanda suka  rushe wadannan abubuwa, a zo ana zargin wanda ya zo zai yi gyara wannan ba a yi adalci ba. “Wadanda suke ganin gwamnatin Buhari ta yi gyara zuwa yanzu, sun fi wadanda suke ganin cewa laifin gwamnatin Buhari ne wannan hali na matsi da ake ciki. Domin ta kawo zaman lafiya, yanzu ana tafiye-tafiye dare da rana ba tare da wata damuwa ba a Najeriya. Yanzu maganar Boko Haram ta yi sauki. Don haka ban yarda cewa gwamnatin Buhari ne ta kawo wa ’yan Najeriya kunci ba, gwamnatin Buhari ta kawo sauki ne ga Najeriya,” inji Sheikh Jingir.Sheikh Jingir ya ce “batagarin da suke yunkurin tayar da darajar Dala a Najeriya, don bata wannan gwamnati, su sani cewa a wurin mu ’yan Najeriya,  tashin Dala ya fi tashin bama-bamai sauki domin tashin Dala abu ne da za a bar mu da rayuwarmu.”
Ya ce muna yi wa gwamnatin Buhari kyakyawan zato kuma mun fara ganin kyakyawan zaton da muka yi mata, musamman ganin irin kokarin da ta yi kan fara samar da zaman lafiya a kasar nan.
Sheikh Jingir ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya kara nuna wa ’yan Najeriya kauna kamar yadda suka nuna masa, ta hanyar gaggauta aiwatar da dukkan abubuwan da ya tsara na kyautata rayuwarsu. Ya yi kira ga talakawan Najeriya, su tausaya wa junansu, su guji zamantowa masu burin samun kudi a jikin ’yan uwansu, ta hanyar gallaza musu. Ya ce “Mu zamanto masu gaskiya masu tunanin yadda za a gina kasar nan.”