Rashin adalci ne a nemi ’yan matan Chibok a wurin Buhari

Wani dan kishin kasa ya ja hankalin ‘yan Najeriya akan cewa su daina yada jita-jita da kuma kokarin yin batanci ga shugabanni. Alhaji Alah Muhammad Katsina ya bayyana wa wakilin Aminiya a Katsina irin takaicinsa akan wasu maganganu da ake yadawa akan cewa, wai iyayen ‘yan matan Chibok da aka sace a lokacin gwamnatin Jonathon […]

Rashin adalci ne a nemi ’yan matan Chibok a wurin Buhari
Rashin adalci ne a nemi ’yan matan Chibok a wurin Buhari

Wani dan kishin kasa ya ja hankalin ‘yan Najeriya akan cewa su daina yada jita-jita da kuma kokarin yin batanci ga shugabanni. Alhaji Alah Muhammad Katsina ya bayyana wa wakilin Aminiya a Katsina irin takaicinsa akan wasu maganganu da ake yadawa akan cewa, wai iyayen ‘yan matan Chibok da aka sace a lokacin gwamnatin Jonathon sunyi nadamar zaben shugaba Buhari akan har yanzu baiyi masu komai ba akan ceto ‘ya’yan nasu daga hannun kungiyar boko haram wadda tayi ikirarin sace su. “Shin wai jama’ar Najeriya sunyi mantuwa ne? Shin ‘yan matan Chibok ne kawai ‘ya’ya?
 Alhaji Ala ya ankarar da jama’ar kasa kan cewa su lura da kyau tun bayan zaben da aka yiwa Buhari a ke yiwa gwamnatin zagon kasa. “ Babban misali a yanzu shine batun rufe kan iyakoki da akayi,maimakon a fahimta dalilin hakan, amma saboda an toshe ma wasu hanyoyin azurta kansu ba tare da tunanin ‘yan kasa ba kullum kalar labarin da zai fito daban amma kuma anki fadin cewa an samu ragowar shigowa da kayan maye ko makamai. Saboda haka,ina ganin rashin adalci ne ace za’a nemi ‘yan matan Chibok ta hannun shugaba Buhari. A yanzu babu abinda ‘yan kasa yakamata suyi illa su cigaba da yiwa kasa da shugabanninta kyakkyawar addu’a. Mu kuma sani,wani bai kawo wa wani tsanani ko samu sai Allah ya kaddara,saboda haka halin da muke ciki kaddara ce daga Allah,sai muyi ta rokonsa gafara da kuma rokon ya yaye mana wannan hali da muke ciki,”inji dan kishin kasa Alhaji Alah Muhammad Katsina.