Rashin adalci ne matsalar Najeriya – Sheikh Isa Jega
Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah na Jihar Kebbi, Sheikh Abdurrahman Isa Jega ya ce shugabancin rashin adalci na babbar matsalar da ke hana zaman lafiya da ci gaban Najeriya da duniya baki daya lamarin da a yanzu ya haifar da zubar da jini da yake-yake a duniya. Sheikh Abdurrahman Isa Jega ya […]
Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah na Jihar Kebbi, Sheikh Abdurrahman Isa Jega ya ce shugabancin rashin adalci na babbar matsalar da ke hana zaman lafiya da ci gaban Najeriya da duniya baki daya lamarin da a yanzu ya haifar da zubar da jini da yake-yake a duniya.
Sheikh Abdurrahman Isa Jega ya bayyana haka ne a hirarsa da Aminiya a garin Jega, inda ya ce rashin jagorancin adalci da amana da nuna rashin gaskiya da cin hanci da rashawa da almudahana da badakala da dukiyar jama’a da shugabanni ke yi ne suka haifar da yunwa da talauci da rashin aikin yi har ake samun tashe-tashen hankula a yankin Arewa da wasu sassan Kudu inda ake garkuwa da mutane.
Sheikh Abdurrahman Jega ya nemi Musulmi su himmatu wajen addu’a don asamu zaman lafiya a Najeriya da sauran kasashen Musulmi da Yahudu da Nasara suka tashi tsaye don hada husuma a kasashen duniya da suka mallaka don amfanin kasashensu.
Shugaban na Izala ya kara da cewa matukar ana son kasa da jama’a su ci gaba, dole kowa ya cire son zuciya, ya sanya kasar a gaba don a samu rayuwa mai inganci kuma ya zamo wajibi jama’a su yi awon gaba da miyagun shugabanni da ke zaluntarsu, musamman a zabe mai zuwa, “kowa ya yi aiki da kuri’arsa ya kuma kare kuri’arsa har zuwa inda za ta yi amfani, idan talaka ya yi haka za a kawar da azzaluman shugabanni da yardar Allah,” inji shi.