Rashin adalci ya kawo dambarwar siyasa a Najeriya – Sheikh Jingir
Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya cewa abin da ya kawo dambarwar siyasar da ’yan siyasar kasar nan suke ciki a halin yanzu, shi ne rashin adalci. Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ’yan […]

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya cewa abin da ya kawo dambarwar siyasar da ’yan siyasar kasar nan suke ciki a halin yanzu, shi ne rashin adalci.
Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Jos a karshen makon jiya, inda ya ce duk wanda yake rike da shugabanci wajibi ne ya rike kowa da adalci ya samar da tsaro ya raya kasa da ayyukan ci gaba. Ya ce amma mafiya yawan ’yan siyasar kasar nan sun yi watsi da wannan nauyi da al’ummar kasa suka dora musu.
Sheikh Jingir ya ce hanyar fita daga wannan hali ita ce ’yan siyasa su gyara halayensu su dawo duk abin da zasu yi su yi tsakani da Allah. Su kuma sauran al’ummar kasa abin da za su yi a matakin zabe na kasa da jiha da kananan hukumomi su zabi mutanen kirki da suka cancanta, don su samu mu fita daga cikin wannan hali.
Sheikh Jingir ya nuna takaici kan yajin aikin da malaman jami’o’in kasar nan ke yi. Ya ce rikici tsakanin malaman jami’o’i da gwamnati da ya kawo yajin aikin wani babban bala’i ne ga kasar nan.
Ya ce yajin aikin yana shafar ’ya’yan talakawa ne kadai, saboda ’ya’yan manya suna ci gaba da karatu a makarantu masu zaman kansu ko a kasashen waje. Ya yi kira ga gwamnati ta dubi koke-koken malaman jami’o’in don kawo karshen yajin aikin.
Dagan an sai Sheikh Jingir ya yi Allah wadai da kashe matasa bakwai da jami’an tsaro suka yi a Unguwar Apo da ke Abuja a ranar Juma’ar da ta gabata da sunan Boko Haram. Ya nemi a kafa kwamiti mai karfi da zai yi bincike tare da kamo jami’an tsaron da suka yi wannan danyyen aiki domin a hukumta su.
Sheikh Jingir ya yaba wa gwamnatin Saudiya da Hukumar Hajji ta kasa, kan shirye-shiryen aikin Hajjin bana. Ya ce yadda aka fara jigilar alhazan Najeriya zuwa Saudiyya, akwai alamun za a samu gagarumar nasara a aikin Hajjin bana. Ya yi kira ga alhazan su yi wa kasar nan addu’ar neman mafita kan halin da take ciki.
Da ya juya kan hadewar kungiyar Izala, Sheikh Jingir ya ce daga lokacin da bangarorin kungiyar suka hade zuwa yanzu sun samu nasarar da ta kai kashi 90 cikin 100.
Ya ce a yanzu duk shugabannin bangarorin kungiyar tare suke komai, babu maganar gaba da juna babu zage-zage kuma ayyukan da suke gudanarwa suna samun nasara fiye da lokacin da kungiyar ke rabe.
Ya ce, “Tunda aka kafa kungiyar ba mu taba samun nasarar gabatar da taron gidauniyar raya ilimi kamar wanda muka gabatar bana a Abuja ba. Haka ba mu taba samun nasarar taron ’yan agajin kungiyarmu, kamar na bana da muka yi a Dutse ta Jihar Jigawa ba. Kuma ba mu taba samun nasarar gasar karatun Alkur’ani ta kasa, kamar wadda muka yi kwanakin baya a Kaduna ba. Muna nan za mu kafa wata babbar makaranta a Kaduna da sakatariya da za a rika gudanar da ayyuka.”