Rashin adalci ya sa ake zagin ’yan fim- Maimuna Wata Yarinya

Maimuna Muhammad, wadda aka fi sani da Maimuna Wata Yarinya, ta dade a harkar fim. Shekara uku da ta gabata an daina jin duriyarta a harkar, daga bisani ta dawo. Ta yi bayanin dalilin da ya sa aka ji ta shiru, sannan ta tabo wadansu batutuwan da suka shafi rayuwarta. A sha karatu lafiya: Za […]

Rashin adalci ya sa ake zagin ’yan fim- Maimuna Wata Yarinya
Rashin adalci ya sa ake zagin ’yan fim- Maimuna Wata Yarinya

Maimuna Muhammad, wadda aka fi sani da Maimuna Wata Yarinya, ta dade a harkar fim. Shekara uku da ta gabata an daina jin duriyarta a harkar, daga bisani ta dawo. Ta yi bayanin dalilin da ya sa aka ji ta shiru, sannan ta tabo wadansu batutuwan da suka shafi rayuwarta. A sha karatu lafiya:

Za mu fara da jin takaitaccen tarihinki.
Assalamu alaikum, sunana Maimuna Muhammad wacce aka fi sani da Maimuna Wata Yarinya. Na yi makarantar firamare da sakandare a garin Maiduguri. Daga nan muka dawo Kano, inda na yi Difloma dina. Har yanzu ina zaune a birnin Kano.
Me ya ja hankalinki kika shiga harkar fim?
Babu wani abu da ya ja hankalina, harkar fim sana’a ce, kowa yakan shiga sana’ar da ya ga ta fi masa. Ka sani Allah ne Yake sa dan Adam a hanyar da zai ci abincinsa. Ban shiga harkar fim don sha’awa ko fadakarwa ba, na shiga harkar ne don ta zama min sana’a. Kuma na rike sana’ar fim da gaske, kamar yadda kowa yake ji da sana’arsa, haka nima nake ji da sana’ar fim.
A kwanakin baya an ji ki shiru, kwatsam sai aka fara ganin ki a sababbin fina-finai, ko me ya jawo hakan?
Gaskiya ne na daina fitowa a fim. Ka sani komai na bukatar hutu, masu magana suna cewa rai dangin goro ne. A baya na yi tafiye-tafiye sakamakon wadansu abubuwa da suka rika taso mini, sannan na yi shekara daya ba na Najeriya, bayan na dawo gida kuma sai na yi hutun shekara daya. A takaice dai na yi hutun shekara kusan hudu ke nan.
Bayan kin dawo gida yaya aka yi kika koma harkar fim?
Gaskiya ko bayan da na dawo ma ban bari ’yan fim da yawa sun san na dawo ba, sai kalilan. Wata rana ina zaune a gida sai Gambo Uban-Tani ya kira ni, bayan na dauka mun gaisa ne, sai yake tambaya ta, ko a ina nake, sai na fada masa ina Kano. Sai ya ce na kwaso kayana in taho Abuja. Na tambaye shi ko lafiya, sai ya ce aiki zan yi da shi. Zan tuna sunan fim din ‘Ina Muka Dosa’, haka na je Abuja. Abin da ya ba ni dariya da mamaki shi ne, a ranar da aka dora mini kyamara sai na ji wani iri, kamar sabuwar shiga. Wannan shi ne yadda na dawo harkar fim bayan hutun da na je.
Bayan an dora miki kyamarar kin ce kin ji kamar sabuwar shiga, to yaya kika yi?
Na sanya kwazo ne kawai, dama ba wai ban san yadda abin yake ba ne, ka san idan ka dauki lokaci ba ka yi abu ba, idan ka dawo za ka ji kamar sabo yake. A haka dai na mayar da hankali muka kammala daukar fim din.
Tun lokacin da kika fara fim zuwa yau ko akwai wani fim da ya fi ba ki wahala?
Gaskiya akwai, wani fim da muka yi  a Lafiya, Jihar Nasarawa, sunan fim din ‘Nurun’. Fim din ya ba ni wahala. Fim ne da aka yi a daji. Ali Nuhu da Shu’aibu Kumurci da kuma ni muka ja fim din. A fim din na yi rol din da ban taba yin irinsa ba.
Zuwa yanzu kin yi fina-finai kamar nawa?
Fina-finan da na yi a da ba zan iya kirga su ba, amma bayan na dawo fim, ina tsammanin na yi fina-finai manya da kanana kamar 30.
Kin dade a harkar fim har ma kin je hutu, yanzu kuma kin dawo, shin kin dawo harkar fim da wani burin da kike so ki cimma?
Yanzu dai ba ni da wani buri, kuma duk inda Allah Ya kai ni zan gode maSa.
Ko akwai kalubalen da kike fuskanta yanzu a harkar fim?
Babban kalubalen da nake fuskanta shi ne daga ’yan kallo, kalubalen kuwa shi ne, har yanzu ’yan fim sun kasa fahimtar mene ne fim. Suna kallon duk rol din da mutum ya yi a fim to haka halinsa yake. Ba haka ba ne, fim ne. Ya kamata masu kallo su gane harkar fim sana’a ce, ba wai kawai a yi fim don a burge ba. Jama’a suna kiran dan fim dan iska, mace kuma karuwa. Hakan ba adalci ba ne. Duk mai zagin dan wani, to wata rana sai an zagi dansa. Ba su san me ’ya’yansu za su yi ba.
A cikin fina-finan da kika yi wanne kika fi so, kuma me ya sa?
Babu fim din da nake ji da shi a halin yanzu kamar fim din ‘Ni Da Ke Mun Dace’, sai kuma ‘Ina Muka Dosa’, ina ji da wadannan fina-finan. Haka ma sauran fina-finan da na yi. Dalilin da ya sa nake son su kuwa shi ne, sakamakon rol din da na taka a cikinsu.
Shin har da fina-finanki na baya, ko iya na yanzu ne?
Har da su din.
A bangaren tufafi wanne kika fi so?
Na fi son tufafin da ’yar Musulmi Bahaushe za ta sa.
Abincin da kika fi so?
Duk abin da na samu ci zan yi, ba ni da wani zabi. Mutum bai san wurin da zai tsinci kansa ba. Idan ka dauki wani abinci kawai da shi z aka rika ci, idan ka je wurin da babu shi yaya za ka yi ke nan?
Wadanne kasashe da garuruwa kika je a dalilin fim?
A dalilin fim na je Ghana, na yi fim kamar uku a can. A garuruwa kuwa na je Abuja da Kaduna da Legas da Bauchi da Lafiya da Neja da sauransu.
Maganar aure fa?
Aure nufin Allah ne, Shi Ya ajiye lokacin da zan yi. Ka sani mutuwa da aure na Allah ne. Ina jiran lokacin da Allah Zai kawo mini ranar aurena. Fatana dai Ya kawo mini miji nagari. Mazan yanzu sai a hankali.
Babu tsayayye ke nan?
Za ka iya tsayar da naka, amma akwai wanda Allah Ya yi maka zabi, shi ya sa ake cewa kana naka Allah Yana naSa.