Rashin adalcin gwamnatin baya ne ya janyo talauci – Abubakar Muhammad
Wani dan kasuwa mazaunin Asaba Malam Abubakar Muhammad ya bayyana cewa ya kamata ’yan Najeriya masu tunani su gane cewa rikita-rikita da tsadar kayan masarufi da talauci da rashin aikin da ’yan hamayya suke kuka a kansu, sun samo asali ne daga lokacin shugabanci na Jam’iyyar PDP da jama’a suka kawar da kuri’arsu. “Don haka […]
Wani dan kasuwa mazaunin Asaba Malam Abubakar Muhammad ya bayyana cewa ya kamata ’yan Najeriya masu tunani su gane cewa rikita-rikita da tsadar kayan masarufi da talauci da rashin aikin da ’yan hamayya suke kuka a kansu, sun samo asali ne daga lokacin shugabanci na Jam’iyyar PDP da jama’a suka kawar da kuri’arsu. “Don haka bai kamata mutanen da suka lalata kasar nan ba, su dawo suna nuna rashin jin dadinsu da wannan gwamnati ta wadda babban aikin da ta sanya a gaba shi ne ta samar da zaman lafiya a kasa, abin da ya gagari wancan gwamnatin ta su.
dan kasuwar, Abubakar Muhammad da ke sayar da atamfofi a garin Asaba fadar Jihar Delta ya yi wannan furucin ne a zantawarsa da Aminiya a wannan makon.
Ya ci gaba da cewa: “Shugabanni a waccan gwamnati sun saki hanyar gaskiya, suka ci gaba da yi wa mutane shugabancin kashin dankali, dukiyar kasa kuma suka mayar da ita tamkar ganima ko gadon gidansu. Sun ci gaba samartakar ’ya’yan bera da wawashe dukiyar kasa suna kaiwa su boye inda bai kamata ba. Kuma wannan duk bai ishe su ba, suka ci gaba da daure wa karya da yaudara gindi tare da bayar da kwangiloli na kashe-mu-raba da su da ’ya’yan gidansu.”
Ya kara da cewa: “Don haka, a ganina gaskiyar lamari duk wata matsala da wadannan ’yan adawa suke son su dora wa wannan gwamnati laifi a kai ba gaskiya ba ne. Duk tsadar rayuwa ko wahalar da ake gani yanzu, waccan gwamnatin ne ummalhaba’isinsu. Amma suke son shafa wa gwamnatin yanzu bakin fenti kuma na tabbatar ’yan Najeriya sun fahimci wannan makircin.”