Rashin adalcin maza: Mata ya dace su shugabanci Najeriya – Daraktan NOA

Daraktan Hukumar Wayar da kan Al’umma ta kasa (NOA), reshen Jihar Gombe, Mista Ado Solomon ya ce rashin adalci na shugabannin kasar nan maza ne ya sa aka sace ’yan matan Chibok, inda ya ce da mace ce Shugabar kasa da hakan ba zai yiwu ba.Mista Ado Solomon, ya ce da a ce mace ce […]

Rashin adalcin maza: Mata ya dace su shugabanci Najeriya – Daraktan NOA
Rashin adalcin maza: Mata ya dace su shugabanci Najeriya – Daraktan NOA

Daraktan Hukumar Wayar da kan Al’umma ta kasa (NOA), reshen Jihar Gombe, Mista Ado Solomon ya ce rashin adalci na shugabannin kasar nan maza ne ya sa aka sace ’yan matan Chibok, inda ya ce da mace ce Shugabar kasa da hakan ba zai yiwu ba.
Mista Ado Solomon, ya ce da a ce mace ce ke shugabanci da daga ranar da aka sace ’yan matan Chibok da yanzu an samo su, amma da yake namiji ne Shugaban kasa sai da aka yi wasu kwanaki sannan aka fara nemansu.
Ado Solomon, ya bayyana haka ne a garin Talasse hedkwatar karamar Hukumar Balanga a Jihar Gombe a lokacin taron kungiyar Matan Tangale Waja (TAWADA) na shekara-shekara.
Ya yi kira ga mata cewa su tsaya sosai wajen ganin sun canja maza daga shugabanci saboda kullum maza na danne su komai za a yi sai a ce su mataimaka ne.
Mista Ado Solomon, ya nemi matan su hada kai musamman matan Tangale Waja wajen fitowa takarar siyasa a mukamai daban-daban domin kada su tsaya baya ana yi ban da su idan an ci zabe a rika ba su shugabar mata ko mataimakiya.
Daraktan ya ce idan za su fito takara su guji siyasar batanci da sa addini ko kabilanci a ciki “Ta haka ne kawai za su ci ribar abin da suke nema, ba su rika cin dunduniyar ’yan uwansu mata ba,” inji shi.
Ya ce rashin kokarin matan ne na fitowa takara ya sa yanzu haka a duk jihar babu mace ko daya a majalisar jiha ko shugabar karamar hukuma ko kansila, sai dai a bangaren aiki da ake da mata biyu manyan sakatarori.
Ya shawarce su cewa su guji bambancin siyasa na PDP ko APC muddin ’yar takara mace ce su rufe ido su zabe ta don ta kare musu ’yanci.