‘Rashin adalcin shugabanni ke haifar da matsalolin Arewa’

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Unguwar Federal Lowcost da ke Bauchi Malam Hassan Usman Zango ya nuna damuwa kan yadda shugabannin Najeriya suka gaza magance matsalolin tsaro da talauci da ke ci gaba da addabar talakawan kasar nan.Limamin ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Bauchi a karshen makon jiya.Liman Hassan […]

‘Rashin adalcin shugabanni ke haifar da matsalolin Arewa’
‘Rashin adalcin shugabanni ke haifar da matsalolin Arewa’

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Unguwar Federal Lowcost da ke Bauchi Malam Hassan Usman Zango ya nuna damuwa kan yadda shugabannin Najeriya suka gaza magance matsalolin tsaro da talauci da ke ci gaba da addabar talakawan kasar nan.
Limamin ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Bauchi a karshen makon jiya.
Liman Hassan ya ce Najeriya kasa ce wacce Allah Ya albarkace ta da dimbin arzikin kasa amma babban cutar da ke damun kasar shi ne miyagun shugabanni wadanda babbar damuwarsu ita ce su wadata kansu da iyalansu da kudin jama’a.
“Don haka ba damuwarsu ba ne su sama wa al’umma kayayyakin inganta rayuwa kamar samar da aikin yi ga matasa ta farfado da manya da kananan masana’antu tare da inganta harkokin tsaro. Wannan zalunci na shugabanni ne ya haifar da matsaloli masu yawa a nan Arewa da suke jawo asarar rayuka da barazana ga makomar rayuwar al’umma.
Malamin ya bukaci shugabanni su ji tsoron Allah su san cewa duk abin da mutum ya aikata a duniya zai amsa tambayoyi daya bayan daya ranar gobe     kiyama.
Game da cutar Ebola da ta shigo kasarb nan, Limamin ya shawarci al’ummar Musulmi su ci gaba da yin addu’o’i na musamman har zuwa lokacin da za a shawo kan cutar da ke neman zama ruwan dare game duniya a Nahiyar Afirka.